Mun raba wa Talakawan Najeriya dala miliyan $300m cikin shekara 4, Gwamnatin Buhari

Mun raba wa Talakawan Najeriya dala miliyan $300m cikin shekara 4, Gwamnatin Buhari

  • Gwamnatin tarayyan Najeriya tace ta rabawa yan Najeriya kudi dala miliyan $300m cikin shekara hudu
  • Shugaban hukumar NASSCO, Mista Apera Iorwa, yace gwamnati ta raba kudaden ne ga talakawa a shirin tallafin N5,000 duk wata
  • Yace nan gaba za'a kara talakawan Najeriya miliyan 8.5 domin su amfana a wannan tsarin duk wata har na tsawon shekara

Abuja - Gwamnatin tarayya ta raba dala miliyan $300m (N123,585,000,000) ga talakawa da masu matsakaicin ƙarfi a tsarin tallafin N5,000 cikin shekara hudu.

Shugaban hukumar NASSCO, Mista Apera Iorwa, shine ya bayyana haka a wata hira da jaridar Punch ranar Lahadi.

Hukumar, wacce ke karkashin ma'aikatar jin ƙai, walwala da jin daɗi, ita ke da alhakin kula da shirin na rabawa talakawa kudaɗen duk wata.

Kara karanta wannan

Shekaru kadan bayan nada shi sarauta, fitaccen basarake ya riga mu gidan gaskiya

Talakawan Najeriya
Mun raba wa Talakawan Najeriya dala miliyan $300m cikin shekara 4, Gwamnatin Buhari Hoto: thecable.ng
Asali: UGC

Mista Iorwa yace:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Shirin rabawa talakawa N5,000 duk wata na gwamnatin tarayya, ya lakume tsabar kudi dala miliyan $300m cikin shekara hudu."

Wane tsari FG ke bi wajen raba kudaden?

Haka nan kuma ya ƙara da cewa magidanta miliyan biyu sun amfana da shirin, kuma aƙalla mutum biyar suke amfana daga kowane gida, jimullan mutum miliyan 10 kenan.

"Wannan abu ne da zai cigaba da gudana, duk wata zaka karbi dubu N5,000, amma sabida wasu dalilai muna biyan N10,000 duk bayan wata biyu."

Gwamnatin tarayya da taimakon bankin duniya ta kirkiri hukumar NASSCO a shekarar 2016 domin ƙara habaka shirin social safety nets a Najeriya, da nufin kawo karshen talauci da samun cigaba.

Bankin duniya ya bada tallafin makudan kudi da suka kai dala miliyan $500m ga shirin tallafi na social safety nets, wanda za'a kammala a watan Yuni, 2022.

Kara karanta wannan

Ka tuna da alkawarin da ka dauka: 'Yan Arewa sun roki Buhari kada ya basu kunya a 2022

Zamu cigaba da shirin har 2024 - FG

Iorwa ya bayyana cewa bankin duniya ya sake amincewa da tallafin dala miliyan $800m domin kara faɗaɗa shirin har zuwa 2024, domin karin wasu yan Najeriya miliyan 8.4 su amfana da tsarin.

"Mun samu nasarar samun ƙarin dala $800m daga bankin duniya domin sake fuskantar hauhawan farashi gadan-gadan."
"Zamu fara shirin raba $800m a watan Fabrairu, za su tafi tare da wanda muke yi a yanzun. Shirin yanzun zai kare a watan Yuni kuma ya kunshi yan Najeriya miliyan biyu.
"Karin kudin da muka samu mu zai cigaba da baiwa waɗan nan mutum miliyan biyun har zuwa 2024, sannan zamu biya karin yan Najeriya miliyan 8.5m N5,000 duk wata na tsawon shekara daya."

A wani labarin kuma mun kawo muku yadda aka kama gwamna a Najeriya da iyalan gidan su baki daya bisa zargin kisan kai

Gwamna Wike na jihar Ribas ya bayyana cewa ba zai taɓa mantawa da halaccin lauya Ukala SAN ba a rayuwarsa.

Kara karanta wannan

Abun bakin ciki: ‘Yan gida daya su biyu sun nitse a ruwa a jajiberin sabuwar shekara

Wike yace akwai lokacin da aka kama shi, mafaifinsa da sauran yan gidansu maza da zargin kisa, amma Ukala ya tsaya musu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel