Rahoto: Yadda 'yan crypto suka tafka asarar triliyoyin kudade a 2021 saboda wasu dalilai

Rahoto: Yadda 'yan crypto suka tafka asarar triliyoyin kudade a 2021 saboda wasu dalilai

  • Masu zuba kudade a harkar crypto a cikin watanni 12 na 2021 sun yi asarar sama da Naira tiriliyan 4.11 daga 'yan damfara a yanar gizo
  • 'Yan damfara a yanar gizo sun tafka satar ne ta hanyar kirkiro wasu tsarukan kasuwancin crypto daban-daban don masu zuba jari su sanya kudadensu
  • Tsabar crypto da ke da sunan shahararren fim na Netflix mai suna Squid Game na daya daga cikin tsarukan da 'yan damfara a yanar gizo suka wawure biliyoyi

Barayi a yanar gizo yanzu suna cin gajiyar tabargazar zuba kudade a kudaden intanet na crypto don yaudarar wadanda ke sha'awar zuba hannun jari a harkar crypto.

Wani sabon rahoto mai taken Crypto Hacks & Scams Report 2021” da Crystal Blockchain ta fitar ya nuna cewa 'yan crypto a wannan shekara ta 2021 sun yi asarar sama da dala biliyan 10 (N4.11 tiriliyan) a fadin duniya.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Buhari ya amince a ɗauki ƙarin 'yan sanda 10,000 aiki a Najeriya

Asarar kudi a duniyar bitcoin
Yadda 'yan crypto suka tafka asarar triliyoyin kudade a 2021 saboda wasu dalilai | Hoto: nairametrics.com
Asali: UGC

Yayin da wani rahoto daga Chainalysis ya nuna cewa adadin kudin da aka rasa ya haura dala biliyan 7.7 na kudin crypto a duniya.

Yadda aka yi asarar kudaden crypto

Dangane da bayanan Crystal, 39% na duk kadarorin da aka sace (a Bitcoin ko BTC) an sace su ne ta hanyoyin musaya na coge, haramtattun hanyoyin musaya, ko kuma kwace daga hukumomin kudi.

Nau'in zambar 'zari ka fece' na haifar da asara a duniyar crypto ne ta hanyar wawashe kudin 'yan crypton da suka yi gaggawan zuba hannun jari sannan daga baya su wayi gari an kwashe kudin.

Wani nau'in kuma ana kiransa "rug pulls" wani sabon nau'in zamba ne inda masu kirkirar kudin crypto za su kirkiri sabon tsaba, suyi watsi da shi ba zato ba tsammani, daga baya sai su sauke shi a kasuwa.

Kara karanta wannan

An damke wani matashin dan bindiga yana kokarin tare hanya, an ceto mutum 10 daga hannunsa

A cewar rahoton Chainalysis kusan 90% cikin dari na dukkan zamba a duniyar crypto an yi su ne ta hanyar 'rug pulls'.

Chainalysis ya kara da cewa:

"Yawan zamba na kudi da ke faruwa a kowane lokaci a cikin shekara ya karu da fiye da 60% cikin dari, daga 2,052 a shekarar 2020 zuwa 3,300 a 2021."

Ga wasu daga cikin zamba da aka tafka a 2021 a duniyar crypto

Rahoton nan ya hada irin barnar da barayi suka yi a duniya crypto a wannan shekara ta 2021 da ke shirin karewa nan kusa.

Poly Network

A watan Agusta 2021, barayi sun yi babban sata na cire kudaden crypto da suka kai dala miliyan 613 a dandalin Poly Network na musanyar kudin intanet.

Sai dai barayin sun dawo da kudin crypto da akalla darajarsa ta kai dala miliyan 260 cikin kasa da sa'o'i 24.

Pancake Bunny

Kara karanta wannan

Labari cikin Hotuna: Yan daba sun kai hari filin gangamin taron jam'iyyar PDP a Zamfara

A ranar 19 ga Mayu, an yi kutse a kafar PancakeBunny, inda barayin yanar gizo suka sace kusan dala miliyan 45.

Bitmart

Barayi a yanar gizo sun sace dala miliyan 196 daga dandalin cinikin crypto na Bitmart, kamfanin ya kira wannan sata da"babban cin zarafin tsaro"

Cream Finance

'Yan damfara sun sace dala miliyan 130 a cikin watan Oktoban 2021. A tun farko a watan Fabrairu, sun sace dala miliyan 37, sai kuma a watan Agusta, dala miliyan 29.

BadgerDAO

Barayin kudin crypto na yanar gizo sun sace akalla dala miliyan 120.3 a wannan kafa ta hanyar yin kutse a ka'idojin kudi na DeFi a kasuwar BadgerDAO.

MonoX

Akalla dala miliyan 31 na crypto aka sace ta hanyar yin kutse a runbum sarkakiyar musayar kudi ta MonoX. An fara gano barnar ne a ranar 1 ga watan Disamban nan.

Squid Game

Miliyoyin daloli sun bace a cikin 'yan mintoci kadan bayan tururuwar 'yan crypto sun tattara zuwa wani sabon kudin crypto mai suna "Squid Game" wanda aka kirkira daga sunan wani fim din kamfanin Netflix.

Kara karanta wannan

Nasara daga Allah: Sojoji sun ragargaji 'yan ISWAP a Yobe, sun kama da dama sun hallaka 7

Cikin kankanin lokaci aka ga kudin ya sauka zuwa sifiri, lamarin da ya karya wasu 'yan crypto da dama.

A wani labarin, 'yan crypto sun tafka babban faduwa a ranar Asabar bayan Bitcoin da wasu tsabobin intanet suka rage darajar sama da dala biliyan daya.

Wannan na faruwa ne yayin da 'yan crypto a duniya suka sayar da tsabobin kudaden intanet don daidaituwa da amintattun hannayen jari yayin da bukukuwan Kirsimeti ke gabatowa.

Bitcoin shine mafi daraja a tsabobin kudaden intanet a daraja ta kasuwa, ya fado da 31.6% daga darajar $69,000 mafi girma a shekarar nan a ranar 10 ga Nuwamba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel