Da dumi-dumi: Hadimin Buhari, Garba Shehu ya warke daga cutar Korona

Da dumi-dumi: Hadimin Buhari, Garba Shehu ya warke daga cutar Korona

  • Hadimin shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce yanzu kam ya warware daga cutar Korona da ya kamu da ita
  • A makon da ya gabata ne aka samu labarin shigar Korona fadar shugaban kasa, inda ta kama wasu mutane da dama
  • Daya daga cikinsu, Garba Shehu ya ce ya warke, ya kuma mika sakon godiya ga wadanda suka masa addu'o'i

Abuja - Yanzu muke samun labarin cewa, babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin yada labarai, Garba Shehu, a ranar Laraba ya ce ya murmure daga cutar Korona.

Garba Shehu dai na daga cikin mataimakan shugaban kasa da suka kamu da annobar Korona a makon da ya gabata.

Hadimin Buhari a harkokin yada labarai Garba Shehu ya magantu kan kamuwa da Korona
Da dumi-dumi: Hadimin Buhari, Garba Shehu ya warke daga cutar Korona | Hoto: Garba Shehu
Asali: Facebook

A sakon da ya wallafa a shafinsa na Facebook ya ce:

“Na gode wa Allah Madaukakin Sarki da ya ba ni saurin murmurewa daga Korona.

Kara karanta wannan

Na warke daga cutar COVID-19, Kakakin Buhari, Garba Shehu

“Addu’o’ina da mutuntawa ina mika su gareku da kuka yi addu’a, ko kira ko aika sakon rubutu kuna bayyana damuwar ku game dani.
"Allah ya sa dukkan 'yan kasarmu maza da matan da ke fama da kwayar cutar su samu nasara kan wannan annoba da dukkan karfinsu kuma su samu lafiya nan ba da jimawa ba."

Korona ta barke a Aso Rock: Garba Shehu, Lai Mohammed, Dogarin Buhari duk sun kamu

A baya kunji cewa, sabuwar nauyin cutar Korona ta barke a fadar Shugaban kasa, Aso VIlla, inda manyan hadiman Shugaba Buhari da manyan jami'an gwamnati suka kamu da cutar.

Premium Times ta bankado cewa sakamakon gwajin da aka gudanar ya nuna cewa akalla manyan na kusa da Buhari guda hudu sun kamu da cutar.

Kara karanta wannan

2021: Manyan al'amura 21 da suka faru a fadar shugaban kasa Buhari

Daga cikinsu akwai Sakataren din-din-din na fadar Shugaban kasa, Tijjani Umar; Dogarin Buhari, ADC Kanal Yusuf Dodo; CSO Aliyu Musa da mai magana da yawunsa, Malam Garba Shehu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel