2021: Manyan al'amura 21 da suka faru a fadar shugaban kasa Buhari

2021: Manyan al'amura 21 da suka faru a fadar shugaban kasa Buhari

Al'amura masu tarin yawa sun faru a gidan shugabancin kasar nan wanda ake kira da Aso Rock, fadar shugaban kasa Muhammadu Buhari, a wannan shekarar.

Wadannan al'amuran sun kasance daga cikin dokoki na hukunci, sun fuskanci caccaka, suka da kuma jinjina daga 'yan Najeriya.

2021: Manyan al'amura 21 da suka faru a fadar shugaban kasa Buhari
2021: Manyan al'amura 21 da suka faru a fadar shugaban kasa Buhari. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Ga wasu daga cikin al'amuran:

Sallamar hafsoshin tsaro

A ranar 26 ga watan Janairu, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sallami hafasoshin tsaron kasar nan tare da nada wasu sabbi bayan kira da ya dinga samu daga masu ruwa da tsaki kan hauhawar rashin tsaro a kasar nan.

Buhari ya saka harsashin gina dogo daga Kano zuwa Maradi

Kara karanta wannan

Babu ruwana da rikicinku na APC a Kano, Shugaba Buhari ya yi fashin baki

A ranar 9 ga watan Fabrairu, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da fara aikin titin dogo na Kano zuwa Katsina zuwa Jibiya zuwa Maradi ta yanar gizo.

An nada Bawa shugaban EFCC

A ranar 16 ga watan Fabrairu, Shugaba Buhari ya nada Abdulrasheed Bawa shugaban hukumar yaki da rashawa da hana yi wa tattalin arzikin kasa ta'annati, EFCC.

Hakan ya biyo bayan dakatar da Ibrahim Magu, tsohon shugaban hukumar da aka yi kan zargin waskar da kudaden da aka samo daga mahandama.

An hana jiragen sama sauka ko tashi a Zamfara

A ranar 2 ga watan Maris, shugaban kasa ya bada umarnin haramta tashi ko saukar jiragen sama a Zamfara tare da hana duk wasu al'amuran hakar ma'adanai sakamakon hauhawar rashin tsaro.

Buhari ya amince da fitar da $1.5bn na gyaran matatar Fatakwal

A ranar 17 ga watan Maris, majalisar zartarwa ta amince da fitar da $1.5 biliyan domin gyaran matatar man fetur ta Fatakwal.

Kara karanta wannan

Buhari ga hafsoshin tsaro: Ku murkushe Boko Haram kafin 2023

An nada Usman Baba Alkali matsayin sifeta janar na 'yan sanda

A ranar Talata, 6 ga watan Afirilu, shugaba Buhari ya amince da nada DIG Usman Alkali Baba a matsayin sifeta janar na 'yan sandan Najeriya.

Ministan lamurran 'yan sanda, Mohammed Maigari Dingyadi, ya sanar da hakan ga manema labaran gidan gwamnati.

Buhari ya sallami Hadiza Bala Usman

A ranar 6 ga watan Mayu, Buhari ya amince da bukatar ministan sufuri, Rotimi Amaechi, kan bincikar shugaban hukumar madatsun ruwa ta Najeriya, Hadiza Bala Usman.

A wata takarda da mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu, ya ce shugaban kasan ya bukaci Hadiza Bala Usman da ta sauka daga kujerar ta domin bayar da damar bincike.

An yi wayar salula 'yar Najeriya

A ranar 9 ga watan Yuni, shugaban kasa ya karba wayar farko da aka yi a Najeriya wacce aka fi sani da ITF daga ma'aikatar masana'antu, kasuwanci da hannayen jari, Otunba Adeniyi Adebayo.

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: Ganduje ya ziyarci fadar Buhari, ya ce gwamnoni suna bukatar taimako

An kaddamar da titin dogo na Legas zuwa Ibadan

A ranar 10 ga watan Yuni, shugaban kasa Buhari ya kaddamar da titin dogo na Legas zuwa Ibadan a tashar jirgin kasa ta Mobolaji Johnson da ke Ebute Metta a jihar Legas.

An bai wa ma'aikatan Villa 42 rantsuwar sirri

A ranar 27 ga watan Yuli, fadar shugaban kasa ta bai wa ma'aikata 42 rantsuwar sirri ta hannun Mai shari'a Hamza Mu'azu na babbar kotun tarayya, a dakin taro da ke fadar shugaban kasan.

Buhari ya amince da fitar da $1.484bn na gyaran matatun Kaduna da Warri

A ranar 4 ga watan Augusta, majalisar zartarwa ta tarayya ta bai wa kamfanonin Messrs Saipem SPA da Saipem Contracting Limited kwangilar gyaran matatun man fetur na warri da Kaduna kan kudi $1.484 biliyan.

Buhari ya rattaba hannun kan dokar PIB

A ranar 16 ga watan Augusta, Buhari ya saka hannu kan sabuwar dokar masa'anatun man fetur.

Kara karanta wannan

'Karin Bayani: An bindige manoma 45 har lahira a Nasarawa, wasu 5,000 sun rasa muhallinsu

Buhari ya amince da sake duba wuraren kiwo a jihohi 25 na kasar nan

A ranar 19 ga watan Augusta, shugaban kasa ya amince da shawarar kwamiti kan sake duba tare da gyara wuraren kiwo 368 a fadin jihohi 25 na kasar nan.

Amincewa da amfani da 5G

A ranar 8 ga watan Satumba, majalisar zartarwa ta tarayya ta amince da tsarin karfin amfani da yanar gizo na 5G.

Erdogan ya ziyarci Aso Rock

A ranar 20 ga watan Oktoba, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karba bakuncin shugaban kasa Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan, a fadarsa

Daga bisani a watan Disamba, shugaba Buhari ya ziyarci Istanbul, babban birnin kasar Turkiyya domin halartar wani taro wanda Erdogan ya karba bakuncinsa.

An kaddamar da eNaira

A ranar Litinin, 25 ga watan Oktoba, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da kudin yanar gizo na babban bankin Najeriya, mai suna eNaira.

NDP ta maye gurbin ERGP

Kara karanta wannan

Sokoto: Tambuwal ya ɗauki mataki kan mawaƙin da ya gwangwaje shugaban ƴan bindiga, Bello Turji, da waƙar yabo

A ranar Laraba, 10 ga watan Nuwamba, majalisar zartarwa ta amince da tsarin cigaban kasa na NDP daga 2021 zuwa 2025 mai karfin hannun jari N348.7 tiriliyan.

Buhari ya karba bakuncin sakataren gwamnatin Amurka

A ranar Alhamis, 18 ga watan Nuwamba, shugaban kasa Buhari ya karba bakuncin Anthony Blinken, sakataren gwamnatin Amurka.

Kamfanin jiragen sama na Najeriya

A ranar Laraba, 24 ga watan Nuwamba, ministan sufurin jiragen sama, Sanata hadi Sirika, ya ce kamfanin jiragen sama na Najeriya zai fara aiki a watan Afirilun shekara mai zuwa bayan amincewar majalisar zartarwa.

Ramaphosa ya ziyarci Aso Rock

A ranar Laraba, 1 ga watan Disamba, shugaban kasa Buhari da Cyril Ramaphosa sun yi jawabin hadin guiwa bayan kammala taro karo na goma na hukumar kasashen Najeriya da South Africa wanda aka yi a Abuja.

Cutar Korona ta yi dirar mikiya a Aso Rock

A jajiberin Kirsimeti ne labarin barkewar cutar korona a fadar shugaban kasan Najeriya ta bazu. An ji cewa wasu daga cikin hadiman shugaban kasan duk sun harbu.

Kara karanta wannan

Dirarsa ke da wuya, Shugaba Buhari ya gana da Shugaban kasar Turkiyya

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel