Manyan tirka-tirka da abubuwan mamaki da aka gani a Majalisar Tarayya a shekarar 2022

Manyan tirka-tirka da abubuwan mamaki da aka gani a Majalisar Tarayya a shekarar 2022

  • Abubuwa da dama sun faru a majalisar dattawa da majalisar wakilan tarayya a cikin wannan shekarar
  • Daga cikin abubuwan da suka faru da suka girgiza kowa shi ne kin amincewa da nadin Lauretta Onochie
  • Bayan shekara da shekaru ana kai-komo, ‘Yan majalisa sun amince da kudirin PIB, har ya zama dokar kasa

Abuja – Jerin abubuwan da suka faru a majalisar tarayyar kasar nan a shekarar nan ta 2021 da za a fita, sun sha bam-bam sosai da yadda 2020 ta kasance.

Daily Trust ta kawo wasu daga cikin manyan abubuwan da suka wakana a wannan shekara. Legit.ng Hausa ta daura da na ta binciken a wannan rahoto.

1. Kudirin gyaran zabe

Kudirin gyaran zabe na cikin abubuwan da suka tada kura, da kudirin ya ki samun karbuwa, sai aka ji an fara shirin bankara matakin da shugaban kasa ya dauka.

Kara karanta wannan

Sabuwar dokar Korona: An hana wuraren ibada da gidajen shakatawa a Abuja taro

2. Cin bashi

A wannan shekara ma dai, majalisar tarayya ta cigaba da amincewa da duk wani rokon neman aron kudi da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gabatar mata.

3. PIB

Wani kudiri da ya jawo sabani shi ne PIB wanda zai kawo gyara a harkar mai. A karshe, kudirin ya zama doka, amma ba yadda mutanen Neja-Delta suka so ba.

Majalisar Tarayya
Majalisar Wakilai na kasa Hoto: @HouseNgr
Asali: Twitter

4. Lauretta Onochie

Daga cikin abubuwan da majalisa tayi da ta ba kowa mamaki shi ne kin amincewa da Lauretta Onochie a matsayin kwamishinar INEC kamar yadda Buhari ya nema.

5. Rufin Majalisa na yoyo

Wani abin kunya har ila yau da ya faru a majalisa a shekarar nan shi ne da aka ga kwanon majalisar tarayya ya na yoyo a lokacin damina duk da kudin da ake kashewa.

Kara karanta wannan

Yadda Gwamnoni 6 suka hana Majalisa juyawa Shugaban kasa baya a kan kudirin gyara zabe

6. Kudirin gyara aikin jarida

‘Yan majalisar wakilan tarayya sun yi kokarin gyara dokar NPC wanda hakan ya jawo kungiyoyin ‘yan jarida irinsu NPO, NPAN, NGE da kuma NUJ duk suka yi ca a kansu.

Kudirin gyara dokar zabe

Sule Lamido ya yi kaca-kaca da APC mai mulki da rinjaye a majalisa, yana ganin da an biyewa ‘Yan Majalisar Tarayya, da kudin da ake kashewa wajen zabe ya karu.

An ji babban jagoran na jam'iyyar PDP a Arewacin Najeriya yana cewa Muhammau Buhari ya yi daidai da ya yi fatali da kudirin gyara zaben da Majalisa ta kai masa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel