A kusan karon farko, rikakken ‘Dan adawa, Sule Lamido ya yabawa matakin da Buhari ya dauka

A kusan karon farko, rikakken ‘Dan adawa, Sule Lamido ya yabawa matakin da Buhari ya dauka

  • Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido ya yi magana game da gyara kudirin zabe a Najeriya
  • Alhaji Sule Lamido yace jam’iyyu ya kamata a bari su zabi duk yadda za su fito da ‘dan takararsu
  • ‘Dan siyasar ya yabi Muhammadu Buhari a kan amincewa da kudirin da majalisa su ka kawo masa

Jigawa - Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido, yace zai fi dacewa a bar jam’iyyu su fitar da tsarin da suke sha’awa wajen tsaida ‘dan takara.

Jaridar Daily Trust ta rahoto Sule Lamido yana cewa bai dace a ce wasu a gefe ba ne za su zabawa jam’iyyun siyasa yadda za su fito a ‘dan takararsu a zabe.

Da yake magana da manema labarai a gidansa da ke Bamaina, garin Birnin Kudu a ranar Lahadi, 26 ga watan Disamba, 2021, Sule ya bada wannan shawara.

Kara karanta wannan

Akwai hannun Gwamnoni wajen kawowa Buhari matsalar tsaro inji Tsohon Shugaban Majalisa

A wannan gaba, tsohon gwamnan ya bayyana cewa kin amincewa da sabon kudirin zabe da shugaba Muhammadu Buhari ya yi, ya wanke shi (Sule).

Babban ‘dan adawan ya nuna matakin da Muhammadu Buhari ya dauka ya yi daidai, duk da cewa ya na cikin wadanda ba su ga maciji da shi a siyasa.

Sule, Shugaba Buhari
Shugaba Buhari da Sule Lamido Hoto: Premium Times da Facebook/Femi Adesina
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kudirin ya ci karo da tsarin mulki - Sule

Lamido wanda ya yi Minista da ‘dan majalisa a baya, ya bayyana cewa sabon kudirin zaben zai kawo matsaloli idan har aka amince da shi ya zama doka.

Daga cikin cikas din da za a fuskanta akwai wahalar da ma’aikatan hukumar INEC wajen sa ido a kan zaben fitar da gwani, da kuma kashe kui masu yawa.

“Yayin da kundin tsarin mulki yake karfafa siyasar jam’iyyu, ya kuma ba jam’iyyun dama su gudanar da harkokinsu yadda hukumar INEC ta tanada.”

Kara karanta wannan

Babu sauran sassauci tsakanin mu da yan bindiga, musamman a arewa, Shugaba Buhari

“Sai yanzu ‘yan majalisar APC su maida kansu masu kula da harkokin jam’iyya, wannan ya nuna yadda APC take neman mafaka, ta rasa yadda za tayi."

- Sule Lamido

‘Dan siyasar yace a mulkin soja, an yi lokacin da Air Marshal Alfa ya zama shugaban da ke sa ido a kan harkokin SDP da NRC, amma a yau hakan ya saba doka.

Tribune ta rahoto Sule yana ba PDP shawarar ta shirya yadda za ta yaki wannan kudiri a kotu.

Za a yi sulhu da Kwankwasiyya a Kano?

Yayin da siyasar Kano ta ke canza salo, tsohon gwamna, Sanata Rabiu Kwankwaso yace ba kowa zai iya fahimtar yadda abubuwa suke wakana ba sai gwani a harkar.

Rabiu Kwankwaso ya fadawa ‘Yan Kwankwasiyya da duk sauran magoya baya su iya bakinsu a game da sha’anin sasantawa da kusoshin siyasar Kano a zaben 2023.

Kara karanta wannan

Ziyarar Maiduguri: Abubuwa 3 da na ke so magajina ya yi idan ya karbi mulki - Buhari

Asali: Legit.ng

Online view pixel