Sojojin Sama Ba Za Su Ɗaga Wa 'Yan Bindiga Ƙafa Ba, In Ji CAS

Sojojin Sama Ba Za Su Ɗaga Wa 'Yan Bindiga Ƙafa Ba, In Ji CAS

  • Air Marshal Isiyaka Oladayo Amao, Babban hafsin sojojin saman Najeriya ya ce dakarunsa ba za su bawa 'yan bindiga dama su rika kai hare-hare ba a arewa
  • Shugaban Sojojin Saman ya bayyana hakan ne yayin taron cin abinci na Kirsimeti tare da dakarun sojojin sama na Operation Hadarin Daji a Katsina
  • Amao ya ce an shirya bikin cin abincin ne domin inganta dankon zumunci da kyakkyawar alakar aiki tsakanin sojojin da kuma tuna wadanda suka rasu a bakin aiki

Katsina - Babban hafsin sojojin sama, CAS, Air Marshal Isiyaka Oladayo Amao, ya ce rundunarsa ba za ta bawa yan bindiga damar su rika kai hare-hare ba a Arewa maso Yamma don inganta rayuwar al'umma, rahoton The Nation.

Kara karanta wannan

Sojoji sun yi kicibis da ‘Yan bindiga a asibiti, sun ki mutuwa a hare-haren da aka kai a Zamfara

Amao, wanda ya yi jawabi yayin taron cin abincin Kirsimeti tare da sojojin Hadarin Daji a Katsina, ya ce dakarunsa za su cigaba da hadin kai da sauran hukumomin tsaro don dakile kallubalen da ke addabar kasar.

Sojojin Sama Ba Za Su Ɗaga Wa 'Yan Bindiga Ƙafa Ba, In Ji CAS
Ba samu bari yan bindiga su runtsa ba, Shugaban Sojojin Saman Najeriya. Hoto: The Nation
Asali: Facebook

Amao, wanda ya samu wakilcin babban kwamandan aikace-aikace, Air Vice Marshal Jack A. Yusuf, ya jinjinawa sojojin bisa jajircewar su wurin yaki da yan bindiga a yankin.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce:

"An shirya bikin cin abincin ne domin inganta dankon zumunci da kyakkyawar alakar aiki tsakanin sojojin da kuma tuna wadanda suka rasu a bakin daga."

Kwamandan Sojojin Saman na Operation Hadarin Daji ya nuna godiyarsa ga CAS din saboda samarwa sojojin abin da suke bukata don yin ayyukansu, The Nation ta ruwaito.

Ya ce sojojin za su cigaba da jajircewa da biyayya ga Rundunar Sojojin ta sama don bada gudunmawarsu yayin atisayen sojoji da ke kokarin samar da tsaro a kasar.

Kara karanta wannan

Nasara daga Allah: Sojoji sun ragargaji 'yan ISWAP a Yobe, sun kama da dama sun hallaka 7

'Yan Ta'adda Dagar Kasar Waje Na Shirin Kai Hari a Abuja

A wani labarin, Hukumar Kula da Shige da Fice na kasa, NIS, ta yi gargadin cewa akwai yiwuwar 'yan ta'adda na kasashen waje su kawo hari a babban birnin tarayya Abuja, Daily Trust ta ruwaito.

Kamar yadda ya ke cikin takardan bayannan gwamnati da aka gano a ranar Alhamis, ana shirin kai harin ne tsakanin ranar 17 ga watan Disamba zuwa ranar 31 ga watan Disamba.

Takardan mai kwanan wata ta ranar 23 ga watan Disamban 2021 na dauke da sa hannun Kwantrola na Immigration, Edrin Okoto.

Asali: Legit.ng

Online view pixel