Bidiyon matar da ta isa wurin bikin murnar cikarta shekaru 50 a akwatin gawa ya janyo surutai

Bidiyon matar da ta isa wurin bikin murnar cikarta shekaru 50 a akwatin gawa ya janyo surutai

  • Wata mata wacce ta bayyana wurin bikin zagayowar haihuwarta ya janyo surutai a kafafen sada zumunta bisa yanayin da ta isa wurin shagalin
  • Mutane sun dinga cece-kuce akan yadda ta je wurin bikin cikarta shekaru 50 a cikin wani akwatin gawa wanda aka hada da gilas
  • Tana isa wurin mutane su ka taya ta fitowa daga akwatin kuma nan da nan aka yi gaggawar mika mata abin magana ta fara waka

Ranar haihuwar mutum rana ce mai ban sha’awa da birgewa a rayuwar dan Adam kuma wannan matar ta nuna wa duniya cewa ba za ta taba mantawa da ranar ba.

Matar ta zama abar caccaka da surutai a ranar shagalin cikarta shekaru 50 da haihuwa bisa yadda ta bayyana a wurin bikin cikin wani akwatin gawa na gilashi.

Bidiyon matar da ta isa wurin bikin murnar cikarta shekaru 50 a akwatin gawa ya janyo surutai
Mata ta iso wurin bikin cikarta shekaru 50 a akwatin gawa, mutane sun magantu. Photo Credit: @gossipboyz1
Asali: Instagram

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A bidiyon wanda shafin @gossipboyz1 su ka wallafa a Instagram, an ga yadda ta isa wurin a cikin akwatin gawa.

Tana isa bakin da su ka je taya ta murna su ka taru don taya ta fitowa daga cikin akwatin gawar.

Take anan aka mika mata abin magana ta hau rera wakoki yayin da jama’a su ke kallonta cike da burgewa

Tsokacin jama’a karkashin bidiyon

goglownatural_skincare ta ce:

“Menene haka wannan matar ta ke yi, da za a ce yanzu za ta mutu zabura za ta yi ta hau koke-koke.”

sharon_jamaican_biafan ta ce:

“Me ye haka kuma ta ke yi, ji wata wauta!"

scopicsgg ta yi tsokaci da:

“Ba zan iya ci gaba da kallon wannan bidiyo zuwa karshe ba, abubuwa su na faruwa a kasar nan fa.”

pappy_horris ya ce:

“Dama ta mutu cikin akwatin gawar ko kuma wasa ta ke yi da Ubangiji.”

Bayan rayuwa cikin daji yana cin ciyawa, yanzu wankan sutturu na alfarma ya ke yi, ana girmama shi a gari

A wani rahoton, wani matashi, Nsanzimana Elie ya kasance a baya ya na zama cikin daji saboda yanayin suffar sa, sannan mutanen kauyen sa har tonon sa su ke yi.

Akwai wadanda su ke kiran sa da biri, ashe daukaka ta na nan biye da shi, kamar yadda Legit.ng ta ruwaito.

Mahaifiyar Elie ta ce Ubangiji ya amshi addu’ar ta na ba ta shi da ya yi bayan yaran ta 5 duk sun rasu, kuma ba ta kunyar nuna shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel