Mutanen Kaduna sun maida martani ga kalaman gwamna El-Rufa'i na aika yan ta'adda lahira

Mutanen Kaduna sun maida martani ga kalaman gwamna El-Rufa'i na aika yan ta'adda lahira

  • Mutanen jihar Kaduna sun nuna goyon bayan su kan kalaman gwamnansu na aika yan ta'adda su gamu da Allah
  • Gwamna El-Rufa'i na jihar Kaduna yace bai amince da wasu tubabbun yan ta'adda ba, kawai a kashe su baki ɗaya
  • A cewar wasu mazauna Kaduna, kalaman El-Rufa'i ba sabon abu bane a kunnuwan mutane, amma fatansu shine a aikata

Kaduna - Shugaban ƙungiyar mutanen kudancin Kaduna, (SOKAPU), Jonathan Asake, a wata hira da Dailytrust ya goyi bayan kalaman El-Rufai na tura yan bindiga lahira.

"Abin da ya kamata mu yi shi ne mu yaƙe su saboda wajibi ne mu kare mutuncin ƙasar mu kuma muna da sojojin da za su iya haka," inji shi.

Mazauna kananan hukumomin Birnin Gwari, Giwa da Chikun a jihar Kaduna sun sadaukar da kansu, za su jagoranci sojoji zuwa maboyar yan bindiga.

Kara karanta wannan

El-Rufai ya tura sako ga 'yan Kaduna, ya ce su gaggauta cika shirin tallafin Korona

Gwamna Elrufai
Mutanen Kaduna sun maida martani ga kalaman gwamna El-Rufa'i na aika yan ta'adda lahira Hoto: Nasir El-Rufai
Asali: Facebook

Sani Ibrahim dake zaune a yankin Fatika, karamar hukumar Giwa, yace:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Wannan maganar (a kashe yan bindiga) ita ce matsayar mu tun a baya. Kamata ya yi a kashe yan bindiga kawai."

Jami'an tsaro su zo mu kai su sansanin yan ta'adda

Abubakar Isma'il, mazaunin Birnin Gwari yace:

"Shi ne abin da muke so tun da daɗe wa, gwamnati da hukumomin tsaro su san maɓoyarsu. Idan ma ba su sani ba, su zo zamu kai su."

Wani shugaban al'umma a ƙauyen Udawa, karamar hukumar Chikun, dake kusa da Birnin Gwari, ya roki El-Rufa'i da Buhari su aikata abinda bakinsu ke faɗa.

"Waɗan nan kalaman ba sabbin abu bane a wurin mu, abin da muke so mu gani a ƙasa," inji shi.

Haka nan wani mazaunin ƙauyen Manini a karamar hukumar Chikun, Samson Manini, yace:

Kara karanta wannan

'Karin Bayani: An bindige manoma 45 har lahira a Nasarawa, wasu 5,000 sun rasa muhallinsu

"Matukar gwamnati zata zage dantse ta ɗauki mataki a kan su, abun zai yi kyau, fatan mu shine duk a kashe su. Ba mu cika son magana kullum yan bindiga na zuwa suna kashe mu ba."

A wani labarin kuma Ana tsaka da jita-jitar tana da ciki Aisha Buhari ta umarci hadimanta su tafi hutu

Matar shugaban ƙasa, Aisha Muhammadu Buhari, ta umarci baki ɗaya ma'aikatan ofishinta su tafi hutu har sai sun ji daga gare ta.

Wannan dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da yan Najeriya ke yaɗa jita-jitar cewa ko matar shugaban tana da juna biyu ne.

Asali: Legit.ng

Online view pixel