Da kyar na shawo kan mahaifina ya bari na fito gasar sarauniyar kyau, Shatu Garko

Da kyar na shawo kan mahaifina ya bari na fito gasar sarauniyar kyau, Shatu Garko

  • Shatu Garko, Sarauniyar kyan Najeriya ta 44 ta bayyana yadda ta gamsar da mahaifinta har ya yarda ta shiga gasar
  • Budurwar mai shekaru 18 ta zama mace ta farko mai sa hijabi wacce ta lashe gasar tun da aka fara a shekarar 1957
  • Ta ce dama mahaifiyarta ta goyi bayanta, daga baya suka taushi mahaifinta shi ma ya yarda kuma ya bata goyon baya dari bisa dari

Shatu Garko, Sarauniyar kyau ta 44 a Najeriya ta shaida yadda ta samu nasarar shawo kan mahaifinta har ya amince ta shiga gasar.

Budurwar mai shekaru 18 ta zama mace ta farko mai hijabi da ta kashe gasar tun da aka fara a shekarar 1957 kamar yadda ta shaida wa The Punch a wata hira da jaridar ta yi da ita.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Hisbah a Kano ta ce dole ta zauna iyayen sarauniyar kyau Shatu Garko

Da kyar na shawo kan mahaifina ya bari na fito gasar sarauniyar kyau, Shatu Garko
Da kyar na shawo kan mahaifina ya bari na fito gasar sarauniyar kyau, Shatu Garko. Hoto daga Punchng.com
Asali: UGC

Kamar yadda tace:

“Mahaifiyata dama tana goyon bayana kuma ta na nuna min ba wani abu mai wahala bane, amma mahaifina ne baya so.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Ya damu don gudun kada su tilasta ni in cire hijabi na ko ins a kayan wanka ko kuma su mayar da ni gefe saboda rufe surar jikina da nayi. Mahaifiyata da ni mun taru muna ba shi baki sannan ya amince, da amincewarsa na yi gasar.”

Ta kara da yadda ‘yan bani na iya suka dinga caccakar ta inda su ka dinga cewa zata kai Boko Haram cikin gasar, Punch ta ruwaito.

A cewarta, mutane sun dinga caccakar ta wasu su na cewa ta koma makaranta ta yi karatu maimakon shiga gasar.

Bayan tambayarta idan ta fuskanci wani kalubale saboda shiga gasar ta amsa da, “Eh, ba ‘yan arewa kadai ba, har wasu daban sun caccake ni. Wasu sun dinga cewa zan bata sunan gasar. Akwai wadanda su ka dinga cewa zan kai ‘yan Boko Haram ko kuma makiyayan Fulani cikin gasar. Kawai share su nayi.”

Kara karanta wannan

Masu yi da gaske: Bidiyon wani mutum yana yiwa matarsa kyautar jirgi ya jawo cece-kuce

Ta kara da bayyana yadda lokacin da ta shiga gasar ba ta yi tunanin za ta ci nasara ba amma ta jajirce da kwarin guiwa har ta samu nasarar.

Garko ta lashe gasar ne a ranar Juma’a, 17 ga watan Disamba inda ta kasance mace ta farko daga Kano da ta bige mutane 17 ta ci nasarar.

An yi gasar ne a jihar Legas kuma ta samu kyautuka kamar N10m, zama a katafaren gida na shekara daya, sabuwar mota da kuma damar tallata kaya da dama.

Sarauniyar kyau: 'Yan Najeriya sun caccaki Hisbah kan yunkurin gayyatar iyayen Shatu Garko

A wani labari na daban, hukumar Hisbah reshen jihar Kano ta na shan caccaka bayan bayyana shirin ta na gayyatar iyayen Shatu Garko, wacce ta lashe gasar sarauniyar kyau a 2021.

Garko mai shekaru 18 wacce ta zama mace ta farko mai Hijabi daga jihar Kano ta lashe gasar wacce aka yi a ranar Juma’a da dare a jihar Legas, Daily Trust ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel