‘Yan bindiga sun ba kauyukan Zamfara wa’adi, sun ce a kawo N37m ko kowa ya dandana kudarsa

‘Yan bindiga sun ba kauyukan Zamfara wa’adi, sun ce a kawo N37m ko kowa ya dandana kudarsa

  • ‘Yan bindiga sun tasa kauyukan karamar hukumar Tsafe a gaba, sun ce dole sai an ba su miliyoyi
  • Wadannan ‘yan bindigan sun bukaci a hada masu Naira miliyan 37 nan da ranar Litinin mai zuwa
  • Wa’adin tara kudin ya shafi kauyuka irinsu Hayin Uda, Ruguza, Dumuyu, Zigau, da kuma Gidan Kado

ZamfaraVangaurd ta rahoto cewa ‘Yan bindigan da suka addabi Bayin Allah a kauyukan Tsafe a jihar Zamfara sunce su tanadi kudi ko kuma a kawo masu hari.

Miyagun ‘yan bindigan sun ba mutanen Bawagauga, Hayin Uda, Ruguza, Dumuyu, Zigau, Mai-Rerai da Gidan Kado nan da Litinin su biya Naira miliyan 37.

Wani rahoto daga majiya mai karfi ya tabbatar da wannan labari, yace mutanen wadannan yankuna sun fara tunanin yadda za su iya nemo wadannan kudi.

Kara karanta wannan

‘Yan bindiga sun fito da Malaman musuluncin da suka sace bayan an biya fiye da Naira miliyan 2

‘Yan bindigan sun kacancana kudin ne ga kauyukan bakwai, aka bukaci kowane su kawo kasonsu.

Yadda za a biya wannan kudi

Rahoton yace mutanen kauyen Bawagauga za su biya N13m, na Hayin Uda za su biya N7m, sai mutanen da ke zaune a kauyen Gidan Kado za su tanadi N6m.

Naira miliyan 4 zai fito daga kauyen Mai-Rerai yayin da aka yankewa kauyukan Ruguza, Dumuyu da Zigau Naira miliyan 2, duk daga nan zuwa farkon makon gobe.

Zamfara
Gwamnan Zamfara, Bello Matawalle Hoto: globaltimes.com
Asali: UGC

Street Journal tace an sanar da jami’an tsaro game da wannan wa’adi na karfi da yaji da aka kakabawa mazauna wannan yanki da ke kilomita 25 zuwa Tsafe.

Jagoran ‘yan bindigan da ke jagorantar ta’adin da ake yi a kauyukan Tsafe, Hassan Bamamu, ya taba sa hannu a yarjejeniyar sulhu da aka yi da gwamnatin Zamfara.

Kara karanta wannan

Mutanen Kaduna sun maida martani ga kalaman gwamna El-Rufa'i na aika yan ta'adda lahira

Manema labarai sun tuntubi mai magana da yawun bakin ‘yan sanda na reshen jihar Zamfara, SP Mohammed Shehu, amma bai amsa kiran waya da sakonni ba.

An taba samun irin wadannan a baya, miyagun suka ce dole a aika masu kudi ko su hallaka mutane. A wasu lokutan, ko an biya kudin, ba a fasa kai hare-hare.

Matsalar tsaro a Imo

An ji cewa matsalar rashin tsaro da ake fama a ita a yau ta sa Gwamnoni sun gagara zuwa sallar gawar surukar tsohon hadimin gwamnan Imo, Rochas Okorocha .

Rochas Okorocha ya ba matasan jihar Imo shawara su guji tada tarzoma, yace idan zaben 2023 ya zo, ku fito ku yi waje da bara-gurbin shugabanni ba tare da fada ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel