IGP ya dauki mataki kan jami'an yan sanda da suka kwace wa matasa Bitcoin na miliyan N22m

IGP ya dauki mataki kan jami'an yan sanda da suka kwace wa matasa Bitcoin na miliyan N22m

  • Sufetan yan sanda na kasa, Usman Alkali Baba, ya bada umarnin bincike kan yan sandan CID da suka kwace wa matasa biyu Bitcoin
  • Ana zargin wasu yan sanda na sashin CID a Legas da tilasta wa matasa da kwace musu Bitcoin da suka kai na miliyan N22m
  • IGP ya kafa kwamitin bincike na musamman, kuma ya umarci jami'an su kai kansu ga kwamitin

Abuja - Sufeta janar na yan sandan ƙasar nan, IGP Usman Baba, ya kirayi wasu daga cikin yan sandan dake aiki a sashin binciken manyan laifuka (CID) reshen jihar Legas.

Ya umarci jami'an su kai kansu wurin kwamitin bincike na musamman dake hedkwatar yan sanda ta ƙasa, Abuja, ranar Talata, bisa zargin kwatar kudin intanet na Bitcoin a hannun wasu matasa biyu.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Jami'an yan sanda sun kama Sarki a Najeriya kan wani zargi

Punch ta rahoto cewa jami'an sun yi amfani da karfin ikon da suke da shi wajen kwace wa matasan Butcoin da ya kai darajar miliyan N22m.

IGP Usman Baba
IGP ya dauki mataki kan jami'an yan sanda da suka kwace wa matasa Bitcoin na miliyan N22m Hoto: tribuneonlineng.com
Asali: UGC

Bisa haka ne shugaban rundunar yan sanda ya ɗauki matakin bincike kan zargin da ake wa jami'an, wanda ya saba wa dokokin hukumar da dama.

IGP ya kafa kwamitin SIP

A wata sanarwa da kakakin yan sanda, Frank Mba, ya fitar ranar Litinin, yace IGP ya kafa kwamitin bincike na musamman (SIP) bisa jagorancin DCP Olaolu Adegbite, domin gudanar da bincike kan lamarin.

Daily Nigerian ta rahoto yace:

"Wajibi a ɗauki wannan matakin biyo bayan rahoton dake yawo a kafafen sada zumunta na zargin hannun jami'an yan sanda wajen kwace wa matasa Bitcoin."

Lamarin wanda ya auku ranar 14 ga watan Disamba ya rutsa da Morakinyo Tobiloba Peter da Yusuf Samson Dayo yayinda suke tuki a kan babbar hanyar Ikoyi/Ajah jihar Legas.

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da 'yan bindiga sun sace sarkin gargajiya da malamin fada

Duk wanda aka taba yi wa haka ya kawo mana rahoto - Yan sanda

Sanarwan ta cigaba da cewa duk wanda ya san makamancin haka ta taba faruwa da shi, ya kawo wa kwamitin cikakken bayani domin gudanar da bincike.

"Muna tabbatar wa yan Najeriya, duk jami'in da aka gano yana da hannu, zai fuskanci hukuncin da doka ta tanazar masa."

A wani labari na daban kuma Jami'an kwastam sun damke babbar kwantena maƙare da makamai a Legas

Yayin da lamarin tsaro ke ƙara taɓarɓarewa a Najeriya, jami'an kwastam sun yi babban nasarar dakile yunkurin shigo da makamai

Jami'an kwastam na Tin Can a Legas sun yi ram da wata kwantema makare da katan-katan na bindigu da aburusai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel