Sojoji sun gallazawa yaron da na haifa azaba, har ya mutu, sun bar ni da makoki - 'Yar Sanda

Sojoji sun gallazawa yaron da na haifa azaba, har ya mutu, sun bar ni da makoki - 'Yar Sanda

  • ASP Mercy Ehima ta ce sojojin kasa su na da hannu wajen mutuwar yaronta, Christian Ehima a Benin
  • Wannan jami’ar ‘yan sanda tace sojoji sun gallazawa yaron na ta azabar da ta yi sanadiyyar mutuwarsa
  • Kakakin sojojin kasa, Janar Onyema Nwachukwu ya yi wa ‘yar sandar raddi, yace ba haka aka yi ba

Delta - Wata jami’ar ‘yan sandan Najeriya a jihar Delta, ta zargi sojoji da hannu wajen kashe mata yaro. Jaridar Premium Times ta fitar da wannan rahoto.

ASP Mercy Ehima tace ‘danta, Christian Ehima, ya fado ne daga motar wasu miyagu da suka yi garkuwa da shi, sai ya zo wajen sojoji ya na neman agaji.

Da Ehima ya bukaci wasu sojoji da ke Benin, jihar Edo su taimaka masa, sai suka ci masa zarafi.

Kara karanta wannan

Nasara: Sojoji sun ragargaji sansanin dan bindiga Bello Turji, sun hallaka da dama

Punch tace a cewar Mercy Ehima, a haka wannan Bawan Allah ya mutu a gadon asibiti da rauni a jikinsa, bayan ya bada labarin duk abin da ya faru da shi.

Wannan lamarin ya faru a ranar Juma’a, 10 ga watan Disamba, bayan marigayin ya shiga wata mota ta masu satar mutane da suka nemi suyi gaba da shi.

Jami’ar ‘Yan Sanda
ASP Mercy Ehima da Marigayi Christian Ehima Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Yadda abin ya faru - ASP Mercy Ehima

“Yaro na ya fado daga mota, a sanadiyyar haka ya shige daji. A cikin jejin ya ci karo da katon maciji, ya tsere har ya iso wajen wasu sojojin kasa.”
“Ya dauka sojojin za su taimaka masa, amma da ya ba su labarin abin da ya faru da shi, sai suka tika shi da kasa, su ka shiga yi masa duka.” – Ehima.

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: Hukumar DSS ta ja kunnen Malaman addini da Sarakuna a kan sakin bakinsu

"Yaro na ba zai dauki bindigar sojoji ba"

‘Yar sandar tace sai da ta tuntubi sojojin a waya, kafin ta kai yaron asibiti. Ehima tace sojojin sun zargi yaron da karbe masu bindiga, wanda da kamar wuya.

“Na san ba zai aikata hakan ba, na roke su ka da su harbe mani yaro, su kace sun fasa harbe shi tun da ni ‘yar sanda ce, sai suka ce in zo in dauke shi.” – Ehima.

Birgediya Janar Onyema Nwachukwu ya yi magana

Jaridar Sahara Repoters tace sojoji sun maidawa wannan jami’ar tsaro martani ta bakin mai magana da yawun sojoji na kasa, Birgediya Janar Onyema Nwachukwu.

Janar Nwachukwu yace wannan yaro ya zo wajen sojojin ne tsirara kamar mai tabin hankali, don haka sojojin kasan suka nemi ‘yanuwansa su kai shi asibiti.

Sojoji sun ce su na da hotuna da bidiyon abin da ya faru, kuma mahaifiyar yaron ta furta giya ya sha.

Kara karanta wannan

Sarkin Sheɗanu: Fitaccen Mai Maganin Gargajiya Na Najeriya Mai Mata 59 Da ƳaƳa Fiye Da 300 Ya Mutu

An yi mace-mace a 2021

Ba sabon labari ba ne cewa manyan mutane da yawa sun kwanta dama tsakanin Junairu da Disamban nan. Daga ciki har da tsofaffin Gwamnoni da Ministoci.

A shekarar nan ne Ministan ‘Yar’adua, Abba Sayyadi Ruma ya rasu a asibitin waje, baya ga irinsu Mama Taraba, Aisha Jummai Alhassan ta rasu a kasar Masar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel