Mama Taraba, Mantu, tsofaffin Gwamnoni, Ministoci, ‘Yan Majalisa 25 da aka rasa a 2021

Mama Taraba, Mantu, tsofaffin Gwamnoni, Ministoci, ‘Yan Majalisa 25 da aka rasa a 2021

  • A shekarar nan ta 2021 da ake shirin fita, an samu mace-macen manyan mutane da-dama a Najeriya.
  • Legit.ng Hausa ta tattaro jerin wasu ‘yan siyasa da masu mulki da suka rasa ransu a shekarar nan
  • Daga cikinsu akwai matan tsofaffin shugabannin kasa, Shehu Shagari da kuma Janar Aguiyi-Ironsi

Tsofaffin Ministocin da suka rasu a shekarar nan sun hada da wadanda suka rike mukamai a mulki soja na farar hula irinsu tsohon Jakada, Bunu Sheriff.

Daga cikin tsofaffin Ministoci akwai

1. Tony Anenih (Tsohon Ministan wasanni)

2. Bunu Sheriff

3. Mahmud Tukur

4. Hussaini Zanwa

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya bayar da auren diyar Sanata Shekarau a Kano

5. Abba Sayyadi Ruma

6. Malami Buwai

7. Bala Ka'oje (Tsohon Ministan matasa da wasanni da Sanata)

8. Dr. Halliru Alhassan (Tsohon Ministan kiwon lafiya)

Irinsu Sanata Jummai Alhassan, Cif Tony Momoh da Lateef Jakande sun rike mukamai da-dama baya ga Minista da suka yi. Akwai gwamnonin soji 3 da suka rasu.

Tsofaffin gwamnonin soja da farar hula

9. Lateef Jakande (Tsohon Gwamnan Legas, tsohon Ministan Abacha)

10. Dominic Oneya (Tsohon Gwamnan soja Kano, tsohon shugaban NFA)

11. Anthony Ukpo (Tsohon Gwamnan soja na Ribas)

12. Adetunji Idowu Olurin (Tsohon Gwamnan soja na Oyo)

Mama Taraba
Marigayiya Mama Taraba Hoto: www.icirnigeria.org
Asali: UGC

Tsofaffin ‘Yan majalisar tarayya:

13. Joseph Wayas (Tsohon shugaban majalisar dattawa)

14. Ibrahim Nasiru Mantu (Tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa)

15. Biyi Durojaiye (Tsohon Sanatan Legas)

16. Hosea Ehinlanwo (Tsohon Sanatan Ondo)

17. Gbenga Aluko (Tsohon Sanatan Ekiti)

18. Nuhu Aliyu (Tsohon Sanatan Neja)

19. Sati Gogwim (Tsohon Sanatan Filato)

20. Haruna Maitala (Tsohon ‘dan majalisar tarayya)

Sauran manyan ‘yan siyasa na kasa:

21. Dr. Adegbola Dominic (Shugaban PDP na jihar Legas)

Kara karanta wannan

Tsohon Gwamnan da ya yi shekara 8 a mulki ya fashe da kuka ya na jawabi wajen jana'iza

22. Dr. Obadiah Mailafia (Tsohon gwamnan CBN)

Matan manyan kasa:

23. Hadiza Shehu Shagari

24. Victoria Jonathan Aguiyi-Ironsiga

Na karshe a jerin na mu, wani dattijo ne wanda ya rike mukamai da-dama a gwamnatin tarayya:

25. Ahmad Joda

Asali: Legit.ng

Online view pixel