Ina kaunar ka amma lokacin daukar mataki ya yi, Najeriya na rugujewa, Ortom ga Buhari

Ina kaunar ka amma lokacin daukar mataki ya yi, Najeriya na rugujewa, Ortom ga Buhari

  • Gwamnan jihar Binuwai, Samuel Ortom, ya yi kira ga shugaba Buhari da ya gaggauta daukar mataki domin Najeriya tana ragargajewa ne a halin yanzu
  • Ortom ya bayyana cewa, yana matukar kaunar Buhari amma a yanzu lokaci ne da ya dace a fada masa gaskiya kuma ya dauka mataki
  • Gwamnan arewan ya ce tabbas Buhari uba ne ga wasu, ga wasu kuwa kaka ne yayin da wasu suke tattaba kunnensa, don haka ya dace ya gane halin da ake ciki

Benue - Samuel Ortom, gwamnan jihar Binuwai, ya ce shugaban kasa kaka ne wanda ya dace ya gane cewa kasar nan rushewa ta ke yi sakamakon al'amuran 'yan ta'adda, TheCable ta ruwaito.

A sakon da ya aike wa shugaban kasa Buhari a ranar Asabar domin taya shi murnar cika shekaru 79 a duniya, Nathaniel Ikyur, sakataren yada labarai na Ortom, ya sanar da cewa gwamnan ya ce rashin tsaron da ya addabi mutane ba shi ba ne alkawarin shugaban kasar yayin da ya hau mulki.

Kara karanta wannan

Sokoto: Tambuwal ya ɗauki mataki kan mawaƙin da ya gwangwaje shugaban ƴan bindiga, Bello Turji, da waƙar yabo

Ina kaunar ka amma lokacin daukar mataki ya yi, Najeriya na rugujewa, Ortom ga Buhari
Ina kaunar ka amma lokacin daukar mataki ya yi, Najeriya na rugujewa, Ortom ga Buhari. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

TheCable ta ruwaito cewa, kamar yadda takardar tace, gwamnan wanda ya ce ya na kaunar Buhari, ya yi kira ga shugaban kasa da ya dauka matakin gaggawa domin tsare kasar nan kafin ya bar kujerarsa.

"Na bi sahun iyalanka, abokai, abokanan siyasa da dukkan 'yan Najeriya domin taya ka murnar cika shekaru 79 a duniya," yace
"Ga wasu, shugaban kasa uba ne, ga wasu kuwa kaka ne yayin da wasu kuwa tattaba kunne sukeg are shi wanda ya dace ya gane cewa Najeriya rushewa ta ke yi sakamakon ta'addancin 'yan bindiga wadanda ke cigaba da tarwatsa tubalin hadin kan kasar nan.
"A kowacce rana, ana yanka jama'a kamar dabbobi a gonakinsu, a gida ko kuma a babbaka su yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa wani wuri. Ga fuskokin 'yan ta'addan tasa a bidiyo amma babu wanda aka kama.

Kara karanta wannan

Fadar Shugaban kasa ta jero tulin nasarorin Shugaba Buhari yayin da ya cika shekara 79

“Tituna sun zama tarkuna inda 'yan kasa ke tsoron bi saboda tsoron kada a sace su ko kuma a kashe su. Wannan budadden sirri ne tunda babu wanda ya tsira a kasar nan."

Gwamnan ya ca tsarin tsaron kasar nan ya lalace kuma 'yan kasa suna rayuwa a cikin tsoro.

"Kada shugaban kasa ya saurari mahaukata wadanda ba su fada masa gaskiya, suna ce masa komai daidai.
“Babu abinda ya ke daidai a Najeriya a halin yanzu shugaban kasa. Dole ne ka dauka matakin gaggawa yanzu domin janye kasar nan daga halin da ta ke ciki kafin lokaci ya kure," yace.

Hotunan yadda Buhari ya yi shagalin cikarsa shekaru 79 a duniya a Turkiyya

A wani labari na daban, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi shagalin cikarsa shekaru 79 a duniya a birnin Istanbul da ke Turkiyya a ranar Juma'a.

A zagaye da wasu daga cikin ministocinsa da 'yan diflomasiyyar Najeriya a Turkiyya, shugaban kasar ya yanka kek mai adon kalolin kasar Najeriya.

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari ba zai iya magance matsalar tsaro a shekara mai zuwa ba, inji minista

Ga wasu daga cikin hotunan shagalin bikin murnar wanda Buhari ya yi tare da wasu ministocinsa da wasu manyan jami'an gwamnati kamar yadda Femi Adesina ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Asali: Legit.ng

Online view pixel