Hotunan yadda Buhari ya yi shagalin cikarsa shekaru 79 a duniya a Turkiyya

Hotunan yadda Buhari ya yi shagalin cikarsa shekaru 79 a duniya a Turkiyya

  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yanka kek a birnin Istanbul na kasar Turkiyya yayin da ya cika shekaru 79 a duniya
  • Kamar yadda Femi Adesina ya wallafa hotunan shugaban kasan da wasu mukarrabansa, an ga kek a gabansa mai launin tutar kasar nan
  • Cike da murna wasu ministoci da mukarraban shugaban kasan suka zagaye shi yayin da suka hada masa bikin murnar ba-zata

Istanbul, Turkiyya - Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi shagalin cikarsa shekaru 79 a duniya a birnin Istanbul da ke Turkiyya a ranar Juma'a.

A zagaye da wasu daga cikin ministocinsa da 'yan diflomasiyyar Najeriya a Turkiyya, shugaban kasar ya yanka kek mai adon kalolin kasar Najeriya.

Ga wasu daga cikin hotunan shagalin bikin murnar wanda Buhari ya yi tare da wasu ministocinsa da wasu manyan jami'an gwamnati kamar yadda Femi Adesina ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Kara karanta wannan

Buhari: Da zarar na kammala wa'adin mulki na zan koma gona ta a Daura in tare

Hotunan yadda Buhari ya yi shagalin cikarsa shekaru 79 a duniya a Turkiyya
Hotunan yadda Buhari ya yi shagalin cikarsa shekaru 79 a duniya a Turkiyya. Hoto daga Femi Adesina
Asali: Facebook

Buhari: Da zarar na kammala wa'adin mulki na zan koma gona ta a Daura in tare

A wani labari na daban, Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce ya na da kudirin komawa gonarsa ta Daura, mahaifarsa da ke jihar Katsina, Daily Trust ta ruwaito.

Shugaban kasa ya furta hakan ne a Istanbul, kasar Turkiyya inda aka shirya masa bikin zagayowar ranar haihuwarsa ba tare da saninsa ba a ofishin jakadancin Najeriya da ke kasar.

Buhari ya na kasar Turkiyya yanzu hakan don halartar wani taro inda har ranar haihuwarsa ta zagayo, ya cika shekaru 79 kenan a ranar Juma’a.

Asali: Legit.ng

Online view pixel