Gwamnatin Buhari na neman bashin N250 billion daga hannun yan Najeriya don gina tituna

Gwamnatin Buhari na neman bashin N250 billion daga hannun yan Najeriya don gina tituna

  • Kawo karshen Satumba 2021, ana bin Najeriya jimillar bashin N38.005tnGwamnatin tarayya na neman karban bashin N250 billion daga hannun yan Najeriya don gina tituna a fadin kasa
  • Gwamnati za ta karbi wannan kudi ne ta tsarin 'Sukuk', wani salon kasuwanci na addinin Musulunci
  • Duk wanda ya baiwa gwamnati bashi cikin kudin da ake nema zai samu ribar 12.80% nan da shekaru 10

Abuja - Ofishin kula da bashin Najeriya DMO ta kaddamar da sabon shirin karban bashin N250 billion na 'Sukuk' domin gina tituna a fadin tarayya.

Wannan shine karo na hudu da gwamnatin tarayya ta fitar da wannan tsari.

Wannan wani bashi ne da kowani dan Najeriya zai iya baiwa gwamnati kuma a biyashi kudinsa gaba baya nan da shekaru 10 da ribar 12.8%.

Kara karanta wannan

Waiwaye a 2021: Haziƙan Ɗaliban Najeriya 4 Da Suka Karya Tarihin Da Ba a Taɓa Zaton Wani Zai Iya Ba

An kaddamar da bada wannan bashi ne ranar Alhamis, 16 ga Disamba kuma za'a rufe ranar 24 ga Disamba, TheCable ta ruwaito.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Gwamnatin Buhari na neman bashin N250 billion daga hannun yan Najeriya
Gwamnatin Buhari na neman bashin N250 billion daga hannun yan Najeriya
Asali: Twitter

Me Gwamnati ke bukata

DMO na kira ga kamfanoni, jama'ar gari, kungiyoyi, da daidaikun mutane su ribaci wannan dama.

Za'a yi amfani da wannan kudi ne wajen ginawa yan Najeriya kayan jin dadi, Gwamnatin ta kara.

Menene bashin 'Sukuk'

A cewar Wikipedia, Sukuk wani tsarin bada bashi ne bisa sharrudan addinin Musulunci.

Gwamnatin Najeriya ta fara karban wannan bashi na N100bn a Satumban 2017 don gidan tituna 25 a fadin tarayya. A 2018, ta sake karban N100bn, sannan N162.557 a 2020.

Kawo karshen Satumba 2021, ana bin Najeriya jimillar bashin N38.005tn

Ofishin Manejin basussukan Najeriya DMO ta bayyana cewa kawo karshen Satumban shekarar nan ta 2021, ana bin Najeriya bashin N38.005tn.

Kara karanta wannan

An karrama dan Najeriyan da mayar da kudi N11m da ya tsinta a Dubai

Wannan na kunshe cikin jawabin da DMO ta saki a shafinta na yanar gizo ranar Talata.

Jawabin yace:

"Bisa al'ada, Ofishin Manejin basussukan Najeriya DMO ta wallafa jimillar basussukan da ake bin Najriya kawo 30 ga Satumba, 2021."
"Wannan ya hada da basussukan gida da na waje, jihohin Najeriya 36 da birnin tarayya."
"Bashin ya zauna a N38.005tn ko $92.626bn kawo karshen rubu'i na 3 na shekarar 2021."

Asali: Legit.ng

Online view pixel