Kogi: Fusattatun jama'a sun banka wa caji ofis wuta, sun halaka dan sanda kan kisan masu zanga-zanga 2

Kogi: Fusattatun jama'a sun banka wa caji ofis wuta, sun halaka dan sanda kan kisan masu zanga-zanga 2

  • Mutane uku ciki har da sifetan ‘yan sanda sun rasa rayukansu sakamakon wani hari da fusatattun matasa suka kai ofishin ‘yan sanda da ke karamar hukumar Yagba ta yamma a jihar Kogi
  • Rundunar ‘yan sandan jihar Kogi a ranar Alhamis ta sanar ta wata takarda da ta saki inda ta ce lamarin ya auku ne da safiyar Talata bayan harin da ‘yan fashi suka kai bankuna 3 a jihar
  • Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, William Aya, ya ce ‘yan sandan sun bazama kamen ‘yan fashi ne inda har suka ci nasarar kama mutane biyu, daga nan ne fusatattun matasan suka isa caji ofis din su na bukatar a saki mutane 2 da aka kama

Kogi - Mutane uku sun rasa rayukansu ciki har da sifetan ‘yan sanda sakamakon wani farmaki da fusatattun matasa su ka kai ofishin ‘yan sanda da ke karamar hukumar Yagba ta yamma a jihar Kogi.

Rundunar ‘yan sandan jihar ta fitar da takarda a ranar Alhamis inda ta bayyana yadda mummunan lamari ya auku a ranar Talata, Thecable ta ruwaito.

Kogi: Fusattatun jama'a sun banka wa caji ofis wuta, sun halaka dan sanda kan kisan masu zanga-zanga 2
Kogi: Fusattatun jama'a sun banka wa caji ofis wuta, sun halaka dan sanda kan kisan masu zanga-zanga 2. Hoto daga punchng.com
Asali: UGC

A cewar ‘yan sandan, matasan sun kai farmakin ne bayan wani fashi da wasu suka kai bankuna uku a Odo-Ere da garin Egbe a karamar hukumar.

Kakakin rundunar ‘yan sandan, William Aya, ya ce ‘yan sandan sun bazama kamen wadanda suka yi fashin inda su ka kama mutane biyu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewarsa sun yi kamen ne da taimakon sauran jami’an tsaro ciki har da mafarauta da ‘yan sa kai inda suka nufi dutsen Oke-Eri inda su ka kama wadanda ake zargin su ke da alhakin fashin.

“Bayan kama su an wuce da su ofishin ‘yan sanda da ke Odo-Ere. Taron fusatattun matasan sun bayyana a ofishin ‘yan sandan su na bukatar a sakar musu mutanen su.

“Duk kokarin da ‘yan sanda suka yi bai yuwu ba inda matasan suka hau hargitsa ko ina, daga nan su ka far wa Sifeta Bamisaye Gbenga sannan su ka ji wa PC Sunday Alechenu rauni.”

The Cable ta gano yadda ‘yan sandan suka yi kokarin watsa taron wanda garin haka ne wani dan sanda ya harba bindiga, ya halaka mutane biyu. Take anan jama’a su ka kashe dan sandan sannan su ka banka wa ofishin ‘yan sandan wuta.

'Yan bindiga sun kai hari ofishin yan sanda, sun saki wadanda aka tsare sun kona motocin sintiri

A wani labari na daban, wasu 'yan bindiga da ba a san ko su wanene ba, a ranar Litinin, sun kai hari hedkwatar yan sanda da ke karamar hukumar Ohaukwu da ke jihar Ebonyi.

A ruwayar SaharaReporters, 'yan bindigan sun kai harin ne misalin karfe 2 na dare inda suka saki dukkan wadanda ake tsare da su a ofishin yan sandan.

Maharan sun kuma kona wasu motoccin sintirin yan sanda sannan wasu jami'an yan sandan sun tsere da raunin bindiga.

Asali: Legit.ng

Online view pixel