Da Dumi-Dumi: Sanata ya bukaci Mala Buni ya ɗage gangamin taron APC na kasa, ya bayyana dalilai

Da Dumi-Dumi: Sanata ya bukaci Mala Buni ya ɗage gangamin taron APC na kasa, ya bayyana dalilai

  • Sanata Orji Kalu, ya yi kira ga shugaban kwamitin rikon kwarya na APC, Mala Buni, ya ɗage gangamin taron jam'iyya na ƙasa
  • Kalu yace duba da rigingimun dake cikin APC wasu har sun je gaban kotu, bai kamata a shirya wannam taron ba
  • A cewarsa kamata ya yi masu ruwa da tsaki su maida hankali wajen sasanta rikicin kafin a gudanar da taro na ƙasa

Abuja - A ranar Alhamis, sanata Orji Uzor Kalu, ya roki kwamitin rikon kwarya na APC ta ƙasa, Gwamna Mala Buni, da mambobin kwamitin shirye-shirye su ɗage babban taron jam'iyya na ƙasa wanda za'a gudanar a watan Fabrairu.

A wasikar da ya aike wa Mala Buni, Kalu ya roki jagororin APC su gudanar da zaɓen fidda ɗan takarar shugaban ƙasa da shugabannin APC na ƙasa lokaci daban-daban a wurin taron.

A cewar Kalu, bai dace APC ta gudanar da babban taron ta na ƙasa ba a lokacin da take fama da rikice-rikecen cikin gida, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Sanata Kalu
Da Dumi-Dumi: Sanata ya bukaci Mala Buni ya ɗage gangamin taron APC na kasa, ya bayyana dalilai Hoto: independent.ng
Asali: UGC

A wasikar mai taken, "Bukatar gaggawa na ɗage baban taron APC," Kalu ya yi gargaɗin cewa yin babban taro a Fabrairu ganganci ne duba da tulin rikicin dake cikin gida.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Meyasa yake neman a ɗage lokacin taro?

A wasikar da ya rubutu, Sanata Kalu ya bayyana cewa tun bayan kammala tarukan APC na jihohi aka samu ɓaraka a mafi yawancin rassan APC.

Yace jam'iyyar APC ta tsage gida biyu a jihohi da dama, kuma wannan ba sabon abu bane a mulkin demokaradiyya amma ya kamata a shawo kan lamarin.

Punch ta rahoto Kalu yace:

"Ya kamata mu tuna cewa watsar da rabuwar jam'iyya ta jawo wa APC faɗuwa zaɓe a jihar Zamfara da Ribas."

"Haka nan kuma tsagewar APC ya jawo mata rashin nasara a wasu jihohi da dama saboda gaza tsayawa a sasanta komai. A matsayinka na shugaba mai son zaman lafiya ba zaka bar haka ta faru ba.

Ya kamata a sake canza lokaci - Kalu

Bugu da ƙari sanatan yace ya wajaba akan duk wani ɗan jam'iyya nagari ya yi kokarin ceto jam'iyyarsa daga rugujewa.

"Saboda wannan ne na rubuta takarda zuwa Ofishinka da sauran mambobin kwamitin rikon kwarya, ku sake duba ranar babban taron APC na ƙasa."
"Zai fi amfani a fara ɗage taron tare da maida hankali kan duk wasu hanyoyin shawo kan matsalolin cikin gida da waɗan da suke gaban kotu.

A wani labarin kuma Tsohon gwamnan Kaduna, Ramalan Yero, Ya bayyana shirinsa na tsayawa takara a zaben 2023

Gabanin zaɓen gwamnan jihar Kaduna dake tafe a 2023, tsohon gwamna, Mukhtar Ramalan Yero, yace zai sake neman ɗarewa kujerar gwamna.

Yero, wanda ya sha kaye a hannun El-Rufai a 2015, yace mutane sun gwada PDP na shekara 16, sun kuma gwada APC na shekara 8.

Asali: Legit.ng

Online view pixel