Tuna baya: Lokacin da Janar Buhari ya daure tsohon Shugaban APC a kurkuku na shekara 44

Tuna baya: Lokacin da Janar Buhari ya daure tsohon Shugaban APC a kurkuku na shekara 44

  • Gwamnatin Muhammadu Buhari ne ta daure Bola Ige da Bisi Akande a kurkuku a shekarar 1984
  • Buhari ya zartar da hukuncin daurin shekara 42 a kan Akande bayan ya yi mataimakin gwamna
  • An tuhumi Cif Akande da Bola Ige da amfani da dukiyar gwamnati wajen azurta jam’iyyarsu ta UPN

A makon jiya ne aka kaddamar da littafin tarihin Bisi Akande. A wajen bikin kaddamarwar, Muhammadu Buhari ya yabi Akande, ya kira shi mai gaskiya.

Mai girma Muhammadu Buhari yace Bisi Akande mutum ne mai daraja wanda bai taba bada cin hanci ba, kuma bai taba karbar cin hancin kowa ba tun da yake.

Abin da mafi yawan mutane ba su sani ba shi ne, Janar Muhammadu Buhari ne ya daure Bisi Akande a lokacin da ya zama shugaban kasa na mulkin soja.

Kara karanta wannan

Matasan Arewa ga Obasanjo: Kai dai ba ka da bakin sukar gwamnatin shugaba Buhari

Jaridar The Cable tace shi karon kansa Akande, ya bada labarin yadda aka daure su a kurkuku bayan sojoji sun yi wa gwamnatin Shehu Shagari juyin-mulki a 1983.

A farkon Junairun 1984, gwamnatin soja ta bada sanarwa a jihar Oyo cewa duk wanda ya rike mukami tsakanin 1979 da 1983, ya kai kan shi ofishin ‘yan sanda.

Buhari da tsohon Shugaban APC
Buhari, Tinubu da Bisi Akande Hoto: @MBuhari
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Bisi Akande ya yi gum kan batun zuwa gidan yari

A dalilin haka Akande wanda ya rike manyan mukamai a gwamnatin Bola Ige ya tafi kurkuku. Sai dai tsohon shugaban na APC bai bayyana wanda ya daure su ba.

Wanda ya yi wannan aiki kuwa shi ne Janar Muhammadu Buhari. Akande bai fito daga gidan yari ba sai a 1986, a lokacin da Ibrahim Babangida ya kifar da Buhari.

Akande yace sun hallara ofishin ‘yan sanda da ke Eleyele tare da manyan ‘yan siyasar UPN da NPN. Kafin a ce komai, sai ga su an garkame su a gidan yarin Kirikiri.

Kara karanta wannan

Farin jinin Shugaba Buhari ya yi mummunan sauka bayan hare-hare da kashe-kashe a Arewa

Cif Akande yace a kirikiri suka hadu da Alex Ekwueme wanda ya yi mataimakin shugaban kasa. Abin mamakin shi ne an tsare Shehu Shagari ne a gidan gwamnati.

A karshe kotu ta yankewa Akande daurin shekaru 42 a gidan maza bisa zargin samunsa da laifi a badakalar da gwamnatin Ige ta tafka domin azurta jam’iyyar UPN.

An ba Akande beli a kan wasu sharuda, da ya saba wadannan sharuda sai aka sake daure shi a kurkuku. Bayan shekaru 37 sai aka ji Akande ya na ta yabawa Buhari.

Tinubu zai yi takara?

Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya zauna da ‘Yan kungiyar Northern Alliance Committee a birnin tarayya Abuja, inda ya bayyana niyyarsa na neman takarar a zaben 2023.

Tinubu yace ya na shawara da mutanensa a kan tsayawa takarar kujerar shugabancin Najeriya. Tsohon gwamnan ya bayyana cewa ba zai ba magoya bayansa kunya

Kara karanta wannan

Yadda Sambo Dasuki ya roki Tinubu, Akande a ba Buhari takara shekaru 10 da suka wuce

Asali: Legit.ng

Online view pixel