'Yan Majalisan Arewa sun sa dole Sanatar Ekiti ta janye kudirin da zai daidaita mata da maza

'Yan Majalisan Arewa sun sa dole Sanatar Ekiti ta janye kudirin da zai daidaita mata da maza

  • Kudirin Biodun Olujimi na daidaita mata da maza a aiki da rabon mukamai ya sha kasa a majalisa
  • ‘Yan majalisa sun ki goyon bayan wannan kudiri yayin da Sanata Biodun Olujimi ta gabatar da shi
  • Wasu Sanatocin Arewa sun nuna cewa wani sashen wannan kudiri ya ci karo da koyarwar musulunci

Abuja - Bayan sabani da rashin fahimta da aka samu wajen tafka muhawara a kan kudirin daidaita maza da mata, an janye wannan kudiri daga majalisa.

Rahoton da ya fito daga jaridar Vanguard a ranar Laraba, 15 ga watan Disamba, 2021, ya bayyana cewa dole Sanata Biodun Olujimi ta janye kudirin da ta gabatar.

Biodun Olujimi ta fito da wannan kudiri ne da niyyar a daidaita mata da maza wajen samun damar aiki. Sai dai ana ganin cewa kudirin ya ci karo da addini.

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: Hukumar DSS ta ja kunnen Malaman addini da Sarakuna a kan sakin bakinsu

Kudirin zai ba mata damar samun mukamai a gwamnati, kuma a rika damawa da su a harkokin rayuwa. Har ila yau kudirin ya shafi maza masu fama da nakasa.

Jaridar tace an yi wa wannan kudiri da taken “A bill for an Act to make provisions for the empowerment of women and gender equality and to establish a legislative framework for the empowerment of women”

Sanatar Ekiti
Sanatar Ekiti ta Kudu, Biodun Olujimi Hoto: www.sunnewsonline.com
Asali: UGC

An kuma: Kudirin ya ki zuwa ko ina

Tun lokacin Bukola Saraki aka yi yunkurin shigo da kudirin amma abin bai yiwu ba. Sanatar ta jihar Ekiti ta sake dawowa da batun a majalisar Ahmad Lawan.

Bayan doguwar muhawara a zaman da aka yi a ranar Talata, dole aka tursasawa Olujimi ta janye kudirin saboda dalilan addinin musulunci da kuma al’ada.

Kara karanta wannan

DSS ta ce jama'a su kula, ana kokarin fara daukar dalibai aikin bindiganci da sace mutane

Sanatar ta Kudancin Ekiti ta koka kan yadda aka ki yin na’am da kudirin na ta, tace burin ta shi ne daina maida mata saniyar ware, kuma a daina ci masu zarafi.

Ra'ayoyin Sanatocin Najeriya

Sanata Yusuf Yusuf mai wakiltar Taraba ta tsakiya yace daidaita maza da mata da ake kokarin yi, ya ci karo da koyarwar Al-Kur’ani da duk Musulmai suke bi.

Shi ma Sanatan Sokoto, Aliyu Wamakko yace ba zai amince da wannan kudiri ba domin ya na kokarin daidaita mata da maza, a maimakon adalci tsakaninsu.

Irinsu Sanata Adamu Abdullahi, Oluremi Tinubu da Bala Ibn Na’Allah sun ce ayi waje da kudirin, amma Sanata Istifanus Gyang da wasu sun nuna goyon bayansu.

Rikicin Hameed Ali da Minista

A makon nan ne aka ji cewa sabon kudirin gyara aikin kwastam zai gwara kan Hameed Ali da Ministar kudi, kasafi da tsare-tsaren tattalin arziki, Zainab Ahmed.

Kara karanta wannan

Jami'an tsaro sun kai farmaki sun kamo 'yan bindiga 30, sun ceto wani sarki da aka sace

Ma’aikatar tattali ta soki garambawul da aka yi wa dokar aikin kwastam na kasa inda ake neman ba hukumar kwastam cin gashin kanta, akasin tsarin da ake kai yau.

Asali: Legit.ng

Online view pixel