Rikici: Ministar Buhari da Shugaban Kwastam, Hameed Ali za su cikin kafar wando daya

Rikici: Ministar Buhari da Shugaban Kwastam, Hameed Ali za su cikin kafar wando daya

  • Gwamnatin tarayya da wasu masu ruwa da tsaki sun soki kwaskwarimar da za ayi wa aikin kwastam
  • Ana kukan cewa sabon kudirin da aka kawo zai ba ma’aikatan kwastam karfi da iko fiye da kima
  • Minista ta fadawa majalisar tarayya cewa bai kamata hukumar kwastam ta rika cin gashin kanta ba

Abuja - Ma’aikatar tattalin arziki, kungiyar MAN, jami’an kwastam da sauran masu ruwa da tsaki sun koka a kan karfin da za a ba hukumar kwastam.

A wani rahoto da Daily Trust ta fitar, an ji cewa ana kuka da sabuwar dokar da ake neman shigo da ita, wanda za ta karawa ma’aikatan kwastam karfi.

Da suka bayyana a gaban majalisar wakilai, masu ruwa da tsakin sun nuna rashin amincewarsu game da kwaskwarimar da aka yi wa dokokin kasa.

Kara karanta wannan

DSS ta ce jama'a su kula, ana kokarin fara daukar dalibai aikin bindiganci da sace mutane

A cewar su, wannan kudiri da aka kawo zai karbe aikin hukumomin gwamnati, ya damka su ga kwastam.

The Nigeria Customs Service (Establishment) Bill, 2021

Da take magana a game da kudirin The Nigeria Customs Service (Establishment) Bill, 2021, Ministar kudi tace ana neman a ba jami’an kwastam ‘yanci.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Rikici: Ministar Buhari da Shugaban Kwastam, Hameed Ali za su cikin kafar wando daya
Ministar kudi, Zainab Ahmed Hoto: @ZShamsuna
Asali: Twitter

Sakataren din-din-din na ma’aikatar kudi, Ali Ahmed ya wakilci Zainab Ahmed a zaman, ya soki kudirin, yace a duk kasashe kwastam ba ta cin gashin kanta.

Ministar tarayyar tace kwastam su na aiki ne a karkashin ma’aikatar kudi da tattalin arziki na kasa. Ahmed tace kudirin ya ci karo da dokoki da tsarin mulki.

Abin da dokar kasa ta ce - Ministar kudi

“NCS ba ta da hurumin da za ta shiga wata yarjejeniya a madadin gwamnatin tarayya ba tare da izinin Minista ko majalisar zartarwar ta FEC ba.”

Kara karanta wannan

Wahalar da ‘Yan Najeriya suke ciki za ta karu a 2022, Minista ta karo sababbin haraji

“Ma’aikatar kudi da kasuwanci ne ke da hurumin da za su shiga yarjejeniyar kasa-da-kasa, ko da a kan abin da ya shafi kwastam.” – Ahmed.

Kokarin gyara mu ke yi ba komai ba inji NCS

Mataimakin shugaban kwastam, David Chikan wanda ya wakilci Hameed Ali a zaman da aka yi, yace su na duba wannan kwaskwarima da aka yi wa dokar.

Akasin abin da Minista ta adawa shugaban kwamitin majalisa, Leke Abejide, Kanal Ali (mai ritaya) yace an kawo wadannan gyara ne domin cigaban kasa

Za a gamu da sababbin haraji a shekarar badi

A jiya aka ji Ministar kudi, tsare-tsare, da kasafin tattalin arziki, Zainab Ahmed, tana cewa mutanen kasar nan za su ga karin haraji a shekarar 2022.

Zainab Ahmed tace akwai bukatar Najeriya ta rage dogaro daga arzikin fetur domin ta iya ayyuka. Kan masana ya rabu a kan wannan shiri da Ministar ke yi.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Gwamna ya kori kwamishinan lafiya saboda yi masa katsalandan

Asali: Legit.ng

Online view pixel