Yadda ‘Yan Sanda ke taimakawa ‘Yan bindiga a Arewa – Shugaban Majalisa yayi tonon silili

Yadda ‘Yan Sanda ke taimakawa ‘Yan bindiga a Arewa – Shugaban Majalisa yayi tonon silili

  • Mataimakin shugaban majalisar wakilai yace wasu jami’an tsaro su na taimakawa ‘yan bindiga
  • Hon. Idris Wase ya kawo labarai da za su sa a zargi ‘yan sanda da taimakawa masu satar mutane
  • ‘Dan Majalisar na Filato yace sai an kama wadanda ake tuhuma da laifi, sai a ji ‘yan sanda sun sake su

Abuja - Mataimakin shugaban majalisar wakilan tarayya, Idris Wase (APC, Filato), ya zargi wasu jami’an tsaro da hada-kai da ‘yan bindigan da ke ta’adi.

Jaridar Premium Times ta rahoto Honarabul Idris Wase, a ranar Talata, 14 ga watan Disamba, 2021, ya na jifan ‘yan sanda da wannan zargi mai nauyi.

Hon. Idris Wase ya yi wannan bayani a lokacin da yake magana a game da harin da ‘yan bindiga suka kai kauyen Pinau, karamar hukumar Wase, Filato.

Kara karanta wannan

Yanzu sai mun hada da noma da tuka motar haya, sannan mu koshi – ASUU tace gari ya yi zafi

‘Dan majalisar ya bada misalan lokuta uku da ‘yan sanda suka saki mutanen da ake zargin ‘yan bindiga ne ko masu garkuwa da mutane ko ma ‘yan fashi.

A cewar Wase, akwai ‘yan sandan da suke kawowa gwamnati cikas wajen yakar miyagu, yace da irin wadannan jami’an tsaro ne ake cutar da yankin Arewa.

Shugaban Majalisa yayi tonon silili
Hon. Idris Wase Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Abin da yake faruwa - Wase

“Jami’an tsaro ba su taimakawa. An sace mai dakin hakimin garinmu – Da aka yi garkuwa da ita, ‘yan banga sun je har Taraba sun kama ‘yan bindigan.”
“Suka ceto matar (hakimin), yanzu maganar da nake yi maku shi ne, jami’an ‘yan sanda sun saki wadannan masu garkuwa da mutanen da aka kama.”
“Na biyu, kwanan nan aka cafke wani da ake zargin ya na hada-kai da ‘yan bindiga, ya amsa laifinsa, har ya na yawo a bidiyo, to shi ma an sake shi.”

Kara karanta wannan

Kano: Ƴan Sanda Sun Kama Sojan Bogi, Zailani-Ibrahim Da Ya Ƙware Wurin Tatsar Masu Keke Napep

An fito da wadanda suka sace yaronmu

Fallasar Wase ba ta tsaya a nan ba, jaridar tace ya bada misali da wani ‘danuwansa da aka dauke a Kaduna, yace ‘yan sanda sun saki wadanda suka sace shi.

Hon. Wase yake cewa wannan ya faru ne wani ‘danuwansa na jini da aka yi garkuwa da shi, aka boye a Birnin Gwari, amma sojoji suka yi nasarar ceto shi.

Ko da ya yi magana da gwamna Nasir El-Rufai, ‘dan majalisar yace sai aka fada masa cewa ‘yan sanda sun jagwalgwala lamarin, an saki wanda ake nema.

Ayi hattara - DSS ta fitar da sanarwa

A makon nan ne aka ji cewa hukumar tsaro na DSS masu fararen kaya sun bankado shirin ‘Yan siyasa na amfani da rashin tsaro wajen tunzura Bayin Allah.

Hukumar DSS tace idanun wasu ya rufe, zaben 2023 kurum suke hange, don haka aka ankarar da jama'a kan biyewa ‘Yan siyasa da sakin baki babu linzami.

Kara karanta wannan

Zaratan 'Yan Sanda Sun Halaka 'Yan Ta'adda 2 a Jihar Kaduna

Asali: Legit.ng

Online view pixel