Yanzu sai mun hada da noma da tukin motar haya, sannan mu koshi – ASUU tace gari ya yi zafi

Yanzu sai mun hada da noma da tukin motar haya, sannan mu koshi – ASUU tace gari ya yi zafi

  • Kungiyar ASUU tace an maida mambobin ta manoma da direbobin motocin haya saboda wahala
  • A ranar Talatar nan malamai masu koyarwa a jami'o'i suka koka a kan yadda aka tagayyarar da su
  • Farfesa Adelaja Odukoya ya caccaki gwamnatin tarayya a kan biyan ‘yan majalisa albashin miliyoyi

Lagos - Kungiyar ASUU ta malaman jami’a ta bayyana cewa mafi yawan ‘ya ‘yanta sun zama manoma da direbobi domin rayuwa tayi masu wahala.

Jaridar Vanguard ta rahoto shugaban ASUU na yankin Legas, Adelaja Odukoya ya na cewa Sanatoci da ‘yan majalisa suna samun albashi mai tsoka.

A lokacin da ‘yan majalisa suke tashi da makudan kudi a kowane wata, Adelaja Odukoya yace gwamnatin tarayya ta bar malaman jami’a a tagayyare.

Odukoya ya yi wannan bayani ne a ranar Talata, 14 ga watan Disamba, 2021, lokacin da ya zanta da manema labarai a jami’ar gona ta FUNAAB a Ogun.

Kara karanta wannan

Idan mu ka tafi yajin-aiki, za a garkame jami’o’i kenan sai illa Masha Allahu - Kungiyar ASUU

Malamin makarantar ya zargi gwamnati da zaluntar malamai a dalilin kin dabbaka yarjejeniyar 2020.

ASUU tace gari ya yi zafi
Motar haya a Legas Hoto: techpoint.africa
Asali: UGC

Albashin malamin jami'a N400, 000 ne

Shugaban na ASUU yace a lokacin da ‘yan majalisa suke karbar tsakanin N1.3m zuwa N1.5m duk wata, Farfesoshi ba su samun abin da ya zarce N416, 000.

Haka zalika kungiyar tace babu abin da zai hana ta tafiya yajin-aikin da ta yi niyya, muddin gwamnatin Muhammadu Buhari ba ta biya mata bukatunta ba.

A cewar Malamin, duk Duniya babu malaman jami’an da ake yi wa karancin albashi irin na Najeriya.

Jawabin shugaban kungiyar na ASUU

“Albashinmu yanzu ba ya isanmu; Mun dade mu na cewa abubuwa sun yi tsada a kasar nan. Amma babu wanda yake cewa komai a Najeriya.”
“A kara albashin malamai ya zama matsala. A lokacin da Ahmad Lawan yace Sanata na karbar N1.5m, ‘yan majalisar wakilai na karbar N1.3m.”

Kara karanta wannan

Ahmad Lawan ya bude sirri, ya fadi albashin sanataoci da 'yan majalisun Najeriya

“Za ku yi mamakin ku ji cewa mafi yawan da ke wajen Legas mu na yin kabu-kabu da sauran ayyuka domin albashinmu ya yi kadan.” - ASUU.

ASUU ta caccaki Ahmad Lawan

Rahoton yace Adelaja Odukoya ya yi wannan magana ne a matsayin raddi ga shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, wanda ya koka game da alawus dinsu.

Kwanaki kungiyar ASUU ta malaman jami’a ta reshen Owerri, tayi barazanar garkame jami’o’i sai lokacin da Allah ya yi, idan suka shiga yajin aiki a shekarar nan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel