Bayan matsin lamba, Buhari ya janye mukamin da ya ba Mai ba shi shawara a Hukumar INEC

Bayan matsin lamba, Buhari ya janye mukamin da ya ba Mai ba shi shawara a Hukumar INEC

  • Shugaban kasa ya amince a nada May Agbamuche Mbu a matsayin kwamishina a hukumar INEC
  • Misis May Agbamuche Mbu ta canji Lauretta Onochie wanda Buhari ya so ta rike wannan mukamin
  • Majalisa ta ki amincewa da hadimar shugaban kasar saboda ana ganin gawurtacciyar ‘yar siyasa ce

Abuja - Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sake nada Malam Mohammed Haruna da May Agbamuche Mbu a matsayin kwamishinonin INEC.

Mohammed Haruna ya na wakiltar Arewa ta tsakiya, yayin da May Agbamuche Mbu ta ke wakiltar Kudu maso kudu a hukumar gudanar da zabe.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa Mai girma Muhammadu Buhari ya zabi May Agbamuche Mbu ta maye gurbin Madam Lauretta Onochie a hukumar.

A shekarar 2020 ne shugaba Buhari ya aikawa majalisa sunan Lauretta Onochie domin a tantance ta. Hakan ya jawo surutu dabam-dabam a fadin Najeriya.

Kara karanta wannan

Farin jinin Shugaba Buhari ya yi mummunan sauka bayan hare-hare da kashe-kashe a Arewa

Onochie na cikin masu ba shugaban kasa shawara, kuma ana yi mata kallon rikakkiyar ‘yar APC da ba ta dace da rike mukami a hukumar shirya zabe ba.

Hadimar Buhari
Lauretta Onochie Hoto: www.channelstv.com
Asali: UGC

Premium Times tace hakan na zuwa ne bayan majalisar dattawa ta ki amincewa da Onochie, ana zargin hadimar shugaban kasar za ta iya son rai a aiki.

Sababbin REC da kwamishinoni a INEC

Baya ga haka, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aikawa majalisar dattawa jerin wasu mutanen da yake so a tantance a matsayin kwamishinoni.

Wadanda ake so a ba mukaman kwamishinonin sun hada da Ukeagu Kenneth Nnamdi, Janar A.B Alkali (rtd), Farfesa Rhoda H. Gumus, da Sam Olumekan.

Sannan an zabi Olaniyi Olaleye Ijalaye a matsayin sabon REC mai wakiltar Kudu maso yamma.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Shugaba Buhari ya naɗa sabon Minista bayan ya kori ministoci biyu daga aiki

Tun a ranar 10 ga watan Disamba, 2021, takardar shugaban kasar ta shiga hannun Sanata Ahmad Lawan, ana sa ran majalisa ta tantance wadanda aka zaba.

PDP da APC sun tara N10bn

A makon da ya gabata aka ji jam'iyyun PDP da APC sun samu sama da Naira biliyan 10 daga harkar saidawa 'yan takara fam tsakanin zaben 2019 zuwa yau.

APC kadai ta tara kusan N7bn wajen saidawa shugaban kasa Muhammadu Buhari, 'yan takarar Gwamnoni da ‘Yan Majalisa fam din tsayawa takara a zaben 2019.

Asali: Legit.ng

Online view pixel