Da Ɗumi-Ɗumi: Rikici Ya Ɓarke a Sabon Garin Kano Tsakanin Ƴan Hisbah Da Matasa
- Rikici ya barke tsakanin unguwar Sabon Garin Kano a daren ranar Talata a yayin da Jami'an Hisbah suka tafi yin kame a Ballat Hughes Road
- Wata majiya ta tsaro ta tabbatar da afkuwar rikicin inda ta ce matasa sun harzuka sun yi ta kone-kone da kai hare-hare inda wasu da dama suka jikkata
- An yi kokari domin ji ta bakin mai magana da yawun yan sandan jihar Kano, Abdullahi Kiyawa, amma hakan bai yi wu ba
Jihar Kano - Rikici ya barke a daren ranar Talata a yankin Sabon Garin Kano a yayin da fusatattun matasa suka tada tarzoma, rahoton Daily Nigerian.
Sabon Gari, yanki ne da mafi yawancin mazauna wurin ba yan asalin jihar Kano bane kuma an saba samun rikici na kabilanci da addini a unguwar.

Asali: Instagram
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Majiyoyi daga hukumomin tsaro sun shaida wa Daily Nigerian cewa rikicin ya fara ne a yayin da jami'an hukumar Hisba suka yi kame a Ballat Hughes Road.
Wani jami'in tsaro ya ce:
"A halin yanzu, ba zan iya fada maka ainihin abin da ya faru ba tsakanin Jami'an Hisbah da matasan. Abin da kawai zan iya cewa shine 'yan Hisbah sun tafi kame sai aka samu matsala, kuma matasa suka fara kai hari suna kona wurare."
Wasu wanda abin ya faru a gabansu sun ce an yi turereniya a Sabon Gari yayin da bata gari suka cinna wuta.
Wasu majiyoyin sun ce an kashe wasu mutane kuma wasu da dama sun jikkata sakamakon rikicin.
Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Kano, Abdullahi Kiyawa, bai amsa kirar da aka yi masa ba domin ji ta bakinsa a kokacin hada wannan rahoton.

Kara karanta wannan
Yanzu-Yanzu: 'Yan Bindiga Sun Sake Kai Hari Masallaci a Neja, Sun Kashe 15 Sun Raunata Da Dama
Kano: Ƴan Sanda Sun Kama Sojan Bogi, Zailani-Ibrahim Da Ya Ƙware Wurin Tatsar Masu Keke Napep
A wani labarin daban, rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta samu nasarar damkar sojan bogi wanda ya kware wurin damfarar masu Napep, The Nation ta ruwaito.
Jami’in hulda da jama’an rundunar, DSP Abdullahi Kiyawa ne ya tabbatar da kamen a wata takarda wacce ya ba manema labarai ranar Talata a Kano.
A cewarsa, wanda ake zargin, Abubakar Zailani-Ibrahim, mai shekaru 27 ya gabatar wa da ‘yan sandan ofishin Rijiyar Zaki kansa a matsayin soja kuma ya je da wani mai Napep.
Asali: Legit.ng