Nnamdi Kanu na cikin walwala da nishadi, babu yunwan da yake ji, DSS tayi martani

Nnamdi Kanu na cikin walwala da nishadi, babu yunwan da yake ji, DSS tayi martani

  • Hukumar DSS ta yi raddi kan jawabin Lauyan Nnamdi Kanu da mambobin kungiyar Biyafara IPOB
  • Sau biyu, Nnamdi Kanu na ikirarin ba'a bashi abinci a hannun hukumar DSS da yake tsare tsawon watanni yanzu
  • Kotu ta baiwa DSS umurni ta bari Nnamdi Kanu yayi duk walwalan da yake so a tsare

Birnin tarayya Abuja - Hukumar tsaron farin kaya, DSS, ta yi watsi da rahotannin cewa shugaban kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu, na shan bakar wahala a hannunta.

Hukumar ta ce zarge-zargen da ake mata ya sabawa dokokin Najeriya da kasashen waje na tsare fursunoni.

Kakakin DSS, Peter Afunanya, wanda ya bayyana hakan ranar Talata a hira da manema labarai a birnin tarayya Abuja ya bayyana cewa Nnamdi Kanu na cikin walwala da nishadi.

Kara karanta wannan

Yadda wani gwamna a Arewa ya kwashi tsabar kudi biliyan N60bn daga lalitar jiharsa, EFCC ta magantu

Yace:

"Hukumar na karyata dukkan zarge-zargen da IPOB keyi kuma a sani Nnamdu Kanu bai cikin wani wahala."
"Kanu na cikin jin dadi da walwala a inda muka tsareshi kuma babu wuri mai kyau irin namu a kasar nan. Ba'a tauye masa wani hakkinsa kuma yana samun ganin Likitoci."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Nnamdi Kanu na cikin walwala da nishadi, babu yunwan da yake ji, DSS tayi martani
Nnamdi Kanu na cikin walwala da nishadi, babu yunwan da yake ji, DSS tayi martani

Kwanan Nnamdi Kanu 3 bai ci abinci ba, Kungiyar IPOB ta laburta

Kungiyar rajin kafa kasar Biyafara IPOB a ranar Asabar ta bayyana cewa hukumar tsaron farin kaya DSS ta hana shugabanta, Nnamdi Kanu, abinci tsawon kwanaki uku yanzu.

IPOB ta bayyana hakan a jawabin da Kakakinta, Emma Powerful, ya saki inda ya bukaci gwamnati ta kai Kanu Kurkuku maimakon wahalan da yake sha hannun DSS.

Kungiyar ta ce tana son duniya ta sani cewa gwamnati na cin zarafin shugabanta Nnamdi Kanu,

Kara karanta wannan

Yadda Manjo Hamza Al-Mustapha ya tserad da ni daga yi mun fyade, Hadimar Buhari

A cewarsa, DSS ta hana shugabansu, Mazi Nnamdu Kanu abinci tsawon kwanaki uku zuwa hudu yanzu.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel