Rahoto: Gwamnati Na Leƙen Asirin Wayoyin Ƴan Adawa, Ƴan Gwagwarmaya, Ƴan Jarida Da Wasu Ƴan Najeriya

Rahoto: Gwamnati Na Leƙen Asirin Wayoyin Ƴan Adawa, Ƴan Gwagwarmaya, Ƴan Jarida Da Wasu Ƴan Najeriya

  • Gwamnatin jihohi da ta tarayya Najeriya su na amfani da kimiyyar leka sakwanni na sadarwar ‘yan Najeriya kamar yadda wani rahoto ya bayyana
  • Rahoton ya nuna cewa hankalin gwamnatin ya fi karkata wurin bibiyar sakwannin ‘yan gwagwarmaya, ‘yan jarida, ‘yan adawar siyasa da sauransu
  • Hakan ya biyo bayan rashin tsaron da ya ke kara yawa a Najeriya don haka gwamnatin ta yanke wannan shawarar don leken asiri

Sabon rahoto ya nuna yadda gwamnati tarayya ta ke amfani da fasaha ta musamman don bibiyar sakwannin da ake tura wa mutum ko ya ke tura wa jama’a ta kafafen sadarwa, The Guardian ta ruwaito.

Wani rahoto daga Action Group On Free Civic Space ya bayyana cewa gwamnati ta na amfani da fasahar ne wurin bibiyar ‘yan gwagwarmaya, ‘yan jarida, ‘yan adawar siyasa da wasu kebantattun mutane.

Rahoto: Gwamnatin Buhari Na Leƙen Asirin Wayoyin Ƴan Adawa, Ƴan Gwagwarmaya, Ƴan Jarida Da Wasu Mutane
Gwamnati na leken asirin wayoyin 'yan Najeriya, Rahoto. Hoto: The Guardian
Asali: Facebook

Manufar rahoton shi ne kawo garanbawul a kan rashin tsaron da ya ke yunkurin raba kawunan jama’an kasa don haka gwamnatin ta sa ido akan ‘yan ta’adda.

NCC ta datse kafofin sadarwa a wasu jihohin arewa

Ma’aikatar sadarwa ta kasa a watan Yunin 2021 ta datse duk wasu kafafen sadarwa a wasu jihohin arewa, Zamfara, Katsina, Yobe da Kaduna sakamakon yadda ‘yan bindiga da sauran ‘yan ta’adda su ka addabi yankin, inda su ka cutar da miliyoyin mutane har fiye da mutane 20,000 su ka rasa rayukansu.

Sai dai The Guardian ta samu rahotanni da ke nuna cewa a boye gwamnatin tarayya ta yi amfani da fasaha ta musamman don sa ido akan jama’a, ‘yan jarida da ‘yan gwagwarmaya ta hanyar a sakwannin sadarwar su.

Duk da dai ba yanzu aka fara zargin gwamnatin ba akan yi wa jama’a leken asiri.

A watan Disamban 2020, hukumar binciken asiri ta sojoji, NDIA, ta mallaki kayan aiki na musamman wadanda za ta iya amfani da su wurin bibiyar waya da sakwanni, kamar yadda University of Toronto’s Citizen Lab ta ruwaito.

Wannan fasahar ta tabbata duk da sukar da ‘yan Najeriya su ka dinga yi a kanta

Kamar yadda sabon rahoton ya nuna:

“Ma’aikatar sadarwa ta jihohi ta yi amfani da damar sabuwar fasahar don bibiyar sakwannin da za su kawo cikas ga tsaron kasa.”

Duk da dai Najeriya ba ta da wata doka ta kare hakkin sadarwar ‘yan kasar ta hana gwamnati bibiyar sakwanni, amma matsalolin da su ke ta barkowa cikin kasar nan kadai sun isa gwamnatin hujjar yin hakan.

A watan Yulin 2021, majalisar dattawan Najeriya ta ware wa NDIA, N4,870,350,000 musamman don kulawa da sakwannin WhatsApp, waya, sakwanni da duk wani hanyar sadarwar dan Najeriya a kasar nan.

Daga N4.8 biliyan, N1.93 bayan wadanda aka ware don bibiyar sakwannin WhatsApp, sai N2.93biyan na Thuraya Interception Solution - hanyar sadarwar da za ta kula da muryoyi ko sakwanni da sauransu.

Dakyar aka amince da wannan bayan yadda mutane su ka dinga sukar abin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel