An yi ram da wani dauke da kan Bil Adama, N25,000 aka saida domin ayi tsafin kudi

An yi ram da wani dauke da kan Bil Adama, N25,000 aka saida domin ayi tsafin kudi

  • ‘Yan Sanda na reshen jihar Oyo sun kama wani mutumi Abideen Raheem da laifin samun kan mutum
  • Abideen Raheem ya amsa laifin da ake zarginsa da shi, yace wani abokinsa ya saidawa kan a N25, 000
  • Da yake tona kansa, Raheem yace a makabarta ya samu wannan kai, ya saida domin ayi tsafin kudi

Oyo - Wani mutumi da ake zargin matsafi ne, Abideen Raheem, ya amsa laifinsa na fito da gawa, ya cire mata kai, kuma ya saida kan ga wani abokinsa.

A ranar Alhamis, 9 ga watan Disamba, 2021, The Nation ta rahoto cewa jami’an ‘yan sandan Najeriya na reshen jihar Oyo, sun damke wannan mutumi.

Abideen Raheem mai shekara 42 ya na cikin mutane 43 da ake zargi da laifuffuka da ‘yan sanda suka kama, kuma suka gurfanar da su gaban ‘yan jarida.

Kara karanta wannan

Bayan shekaru 2 ana wahala, Bill Gates ya fara hango karshen annobar annobar COVID-19

Da yake magana da manema labarai a Ibadan, Raheem yace ya saida kan ne ga abokinsa a kan N25, 000.

‘Yan Sanda sun yi ram da wani da kan Bil Adama, N25,000 aka saida domin ayi tsafin kudi
'Yan Sandan Najeriya Hoto: dailypost.ng
Asali: UGC
“Ina so in taimaki aboki na ne, wanda ya fada mani cewa yana neman kan mutum domin ya yi tsafin yin kudi.”
“Sai na yanke kan da wuka, na dauka na kai wa abokin nawa da ya fada mani yana bukata ya yi tsafi.” – Raheem.

A ina ya samo kan mutum?

Jaridar ta rahoto Raheem ya na bayanin yadda ya je wata makabarta a garin Ibadan, ya samo wannan kai ya saida, daga baya sai aka kama abokin na sa.

“Na ciro gawa daga wata makabarta a yankin Olunde a garin Ibadan a ranar Asabar. Ina samun kan, na kira aboki na, Moruf Ganiyu ya zo ya dauka.”

Kara karanta wannan

Wallafar da Naziru Sarkin waƙa ya yi akan dukan mata ta janyo cece-kuce

“An kama shi (Moruf Ganiyu) ne da kan, yayin da yake hanyarsa ta zuwa gida. Damke shi da aka yi ne ta sa ni ma aka yi ram da ni.” - Abideen Raheem.

Kwamishinar ‘yan sanda ta jihar Oyo, Ngozi Onadeko tace za a gurfanar da wadannan mutane da zargin samunsu da amfani da kan mutum ba tare da ka’ida ba.

Neman halal da wuya

A yau kun ji labarin wani Bawan Allah Mai hannu daya da ya kware a aikin faskare. Kabiru Alhassan yace ya na yin aikin da masu hannu ba za su iya ba.

Duk da hannun Kabiru Alhassan daya, idan ya rike gatari zai yi aikin da karfafa ba za su iya ba. A haka wannan mutumi ya yi aure, yanzu ya na da 'ya 'ya hudu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel