EFCC na neman ‘dan kasuwan da ya tsere da sama da Naira biliyan 200 daga hannun mutane

EFCC na neman ‘dan kasuwan da ya tsere da sama da Naira biliyan 200 daga hannun mutane

  • Hukumar EFCC ta bada cigiyar Mista Maxwell Odum bayan ya tsere da kudin dubunnan mutane
  • A wata sanarwa da EFCC ta fitar a makon nan, tace ta na zargin Odum da satar Naira biliyan 213
  • An bukaci duk wanda ya ji labarin inda wannan ‘dan kasuwa ya shiga, ya sanar da jami’an tsaro

Lagos - A shafinta na Facebook, EFCC mai yaki da almundahana ta sa Maxwell Odum a cikin jeringiyar mutanen da ta ke nema a dalilin zargin sata.

Hukumar EFCC ta na neman Mista Maxwell Odum, wanda shi ne shugaban kamfanin nan na MBA Capital and Trading Limited masu harkar canji.

Hukumar ta EFCC ta na zargin wannan ‘dan kasuwa da satar kudin da sun kai Naira biliyan 213.

A ranar Laraba, 8 ga watan Disamba, 2021, EFCC ta fitar da sanarwa ta musamman, ta na kira ga jama’a su kawo mata labarin a duk inda suka ga Odum.

Kara karanta wannan

Bayan shekaru 2 ana wahala, Bill Gates ya fara hango karshen annobar annobar COVID-19

A sanarwar da mai magana da yawun bakin hukumar ya fitar, Wilson Uwujaren yace ana zargin wannan ‘dan kasuwa da cin kudi ta hanyar karya da sata.

Hukumar EFCC
EFCC na bidar Maxwell Odum Hoto; @officialefcc
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

EFCC na bidar Maxwell Odum

“Ana sanar da al’umma cewa EFCC ta na neman MAXWELL CHIZI ODUM ko kuma MBA TRADING AND CAPITAL INVESTMENT LIMITED, wanda aka ga hotonsa a nan sama, bisa zargin kutun-kutun, karbar kudi da damfara da satar abin da ya kai N213,000,000,000.00.
“Odum mutumin Ikwerre ne a karamar hukumar Obio-Akpor, jihar Ribas.”
“Ganin da aka yi masa karshe si ne a gida mail amba 7, layin Odum, unguwar Elekahia, garin Fatakwal, jihar Ribas.”
“Duk wanda yake da wani bayani a game da inda ya shiga, ya taimaka ya tuntubi hukumar a ofisoshinta da ke Benin, Kaduna, Ibadan, Sokoto, Gombe, Maiduguri, Makurdi, Ilorin, Enugu, Kano, Legas, Gombe, Fatakwal da Abuja…ko ya je ofishin ‘yan sanda mafi kusa, ko wasu jami’an tsaro.” -EFCC

Kara karanta wannan

An gurfanar da mutumin da aka kama da ATM 2,863 a Legas

Rahoto daga The Cable yace Odum ya tattara kudin mutane da nufin za a juya, sai ya yi gaba. Tun a 2020 aka rufe kamfaninsa da sunan za a tafi hutu, har yau shiru.

An kama wani dauke da ATM 2, 300

A jiyan ne kuma aka ji cewa hukumar EFCC ta gurfanar da wani mai suna Ishaq Abubakar da aka kama da katin ATM 2,683 a filin tashin jiragen sama da ke Legas.

Lauyoyin EFCC sun gurfanar da shi a gaban kotun tarayya da ke garin na Legas ne kan tuhumarsa da ake yi da aikata laifuka 11 masu alaka da damfara ta yanar gizo.

Asali: Legit.ng

Online view pixel