Matashi ya yi shigan soja, ya dura ofishin 'yan sanda ya lakadawa Constable duka

Matashi ya yi shigan soja, ya dura ofishin 'yan sanda ya lakadawa Constable duka

  • Sojan bogi ya dura ofishin 'yan sanda, inda ya samu wata Contable ya lakada mata duka a gaban jami'ai
  • Lamarin ya jawo an kama shi, yanzu haka dai yana tsare a ofishin 'yan sanda inji sanarwar hukumar 'yan sandan Kenya
  • An ce matashin mai shekaru 27 ya dura ofishin da dare, inda ya aje motarsa ya shiga cikin ofishin kai tsaye

Kenya - An kama wani matashi dan kasar Kenya mai shekaru 27, George Onderi bayan da ya kai hari ofishin ‘yan sanda na Suneka, inda ya yi ikirarin cewa shi Sajan din ‘yan sandan soji ne.

Matashin da ya isa ofishin ‘yan sandan da misalin karfe 9 na dare, ya zo ne a mota kirar Toyota Belta, inda ya ki bayyana kansa ga mataimakin OCS sannan ya wuce ciki kai tsaye.

Kara karanta wannan

Kafin a birne shi, ‘Yan Sanda sun samu wani da hannu a kashe Kwamishinan Katsina

Sojan bogi da ya daki Constable
Matashi ya yi shigan soja, ya dura ofishin 'yan sanda ya lakadawa Constable duka | Hoto: National Police Service
Asali: Facebook

An ce ya yi kan wata Constable mai suna Mary Maina a lokacin da yake sanye da kayan sojoji. Onderi "da karfi" ya ci zarafin 'yar sandar, lamarin da ya kai ga sauran abokan aikinta sa baki.

Nan take aka kama shi bayan da ya kasa bayyana waye shi, kuma yanzu haka yana tsare a ofishin yana jiran cikakken bincike daga jami’an DCI.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wani bangaren sanarwar da rundunar ta fitar a shafin Facebook na National Police Service ya ce:

"Jami’an ‘yan sanda a Kisii na tsare da wani mutum da ake zargi da kai farmaki ofishin ofishin ‘yan sanda na Suneka yana sanye da kayan wani Sajan na ‘yan sandan Soja tare da farmaki wata ‘yar sanda da ya yi zarginta da sanya da rigar ‘yan sanda da bai dace ba."

Kara karanta wannan

Bayan shekaru 2 ana wahala, Bill Gates ya fara hango karshen annobar annobar COVID-19

Hakazalika, sanarwar ta kara da bayyana cewa, ba wannan ne karon farko ba, an sha samun mutane na shigar jami'an tsaro suka cin zarafin jami'ai da sauran jama'a.

'Yan sanda sun shiga damuwa bayan jin shuru na albashin Nuwamba

A Najeriya kuwa, jami’an ‘yan sandan Najeriya har yanzu ba su samu albashin watan Nuwamba ba, sakamakon zargi kan wasu ma’aikatan ma’aikatar kudi, kasafin kudi da tsare-tsare ta kasa suka yi na gudanar da biyan kudaden.

Dangane da wannan al’amari, hukumar ‘yan sanda ta kai dauki domin kwantar da tarzoma daga wanda ke korafin rashin biyansu albashi mako guda kenan a watan Disamba.

Punch ta tattaro cewa ‘yan sanda yawanci suna karbar albashi ne a ranar 25 ga kowane wata amma abin da ya faru a yanzu na kara haifar da damuwa a cikin ‘yan sandan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel