Yanzu-Yanzu: An samu karin mutum uku ɗauke da sabon nau'in cutar Omicron a Najeriya

Yanzu-Yanzu: An samu karin mutum uku ɗauke da sabon nau'in cutar Omicron a Najeriya

  • Hukumar NCDC ta tabbatar da sake samun masu ɗauke da nau'in COVID19 na Omicron har mutum uku
  • NCDC tace waɗan da aka gano na ɗauke da sabon nau'in cutar ba su jima da dawowa daga ƙasar South Africa ba
  • A cewar hukumar zata cigaba da aikinta na sanya ido da gano matafiyan dake shigowa Najeriya masu ɗauke da cutar COVID19

Abuja - Hukumar kula da yaduwar cututtuka ta kasa (NCDC) ta tabbatar da sake gano masu ɗauke da sabon nau'in COVID19 na Omicron a Najeriya.

A wata sanarwa da hukumar NCDC ta fitar, ta bayyana cewa an gano cutar ne a jikin wasu mutum uku da suka ziyarci ƙasar South Africa a baya-bayan nan.

Dailytrust ta rahoto cewa bayan samun waɗan nan mutum uku, alkaluman masu ɗauke da sabon nau'in cutar yanzu ya kai mutum 6 a Najeriya.

Kara karanta wannan

Buhari ya kai wasika majalisa, ya nemi a amince da kudirin kudin 2021 kafin 2022

Nau'in Omicron
Yanzu-Yanzu: An samu karin mutum uku ɗauke da sabon nau'in cutar Omicron a Najeriya Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Ya hukumar NCDC ta ɗauki lamarin?

Wani sashin sanarwan yace:

"Hukumar NCDC ta hanyar ɗakin gwaje-gwaje na ƙasa (NRL) na cigaba da kokarin gano masu ɗauke da cutar COVID19 daga matafiyan ƙasa da ƙasa dake shigowa Najeriya."
"Wannan ya kunshi jerin waɗan da ta gano dauke da cutar daga matafiya tun daga watan Oktoba zuwa yau."
"Nau'in Delta ne aka fi yawan samu a yanzu, har yanzun Omicron ba ta maye gurbinta ba kamar yadda abun ke faruwa a wasu kasashen."

Omicron ta zama barazana a Duniya

NCDC ta bayyana cewa sabon nau'in korona na Omicron ya zamaa barazana kuma abin damuwa a duniya saboda hatsarinta na saurin yaɗuwa.

"Kamar yadda ake ɗauka, idan dagaske ne, nau'in Omicron ya canza akalar yanayin yaɗuwar cutar COVID19. Babu cikakkiyar shedar cewa sabon nau'in ya watsu sosai a yankunan Najeriya."

Kara karanta wannan

Buhari ya kori shugabannin wutan lantarki a Abuja saboda yajin aikin ma’aikata

Hukumar ta sanar da bullar sabon nau'in Omicron na farko a ranar 1 ga watan Disamba, 2021, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

A wani labarin na daban kuma Hukumar NHRC zata binciki mummunan kisan da akai wa Fulani a jihar Edo

Hukumar kare hakkin bil adama ta ƙasa (NHRC) ta sha alwashin gudanar da bincike kan kisan Fulani a jihar Edo.

Sakataren hukumar, Tony Ojukwu, yace lamarin ya munana sosai, kuma duk me hannu a kisan zai girbi abinda ya shuka.

Asali: Legit.ng

Online view pixel