Buhari ya kori shugabannin wutan lantarki a Abuja saboda yajin aikin ma’aikata

Buhari ya kori shugabannin wutan lantarki a Abuja saboda yajin aikin ma’aikata

  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ba da umarnin korar wasu manyan jami'ai a kamfanin rarraba wutar lantarki ta Abuja
  • Hakan ya biyo bayan wani yanjin aiki da ma'aikatan kamfanin suka yi a kwanakin nan, wanda ya jawo daukewar wuta
  • Gwamnatin Buhari ta ba da umarnin tsige shugabannin gudanarwar kamfanin, tare da biyan ma'aikata hakkinsu

Abuja - Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da korar shugabannin Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki ta Abuja (AEDC) sakamakon yajin aikin da Kungiyar Ma’aikatan Wutar Lantarki ta Najeriya (NUEE) ta yi.

Yajin aikin da NUEE ta yi ya bar yankunan da AEDC ke kula dasu ba wutar lantarki na tsawon sa’o’i a ranar Litinin.

Shugaban Najeriya, Buhari
Yanzu-Yanzu: Buhari ya kori shugabannin wutan lantarki a Abuja bisa yajin aikin ma’aikata | premiumtimesng.com
Asali: UGC

Wasu daga cikin yankunan da kamfanin ke ba wuta sun hada da babban birnin tarayya (FCT), jihar Kogi, Nasarawa da kuma jihar Neja.

Kara karanta wannan

Hukumar NUC ta bankado wasu jami’o’i da makarantun bogi 67 da ke bada satifiket

Ma’aikatan sun yi zanga-zangar rashin biyansu alawus, albashi da kuma rage musu kudaden fensho.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wata sanarwa da Ofem Uket, mai taimaka wa karamin ministan wutar lantarki kan harkokin yada labarai ya fitar a ranar Talata, ta ce shugaban kasar ya amince da sabuwar hukumar riko da za ta kula da harkokin yau da kullum na kamfanin.

A cewar sanarwar:

“Kamar yadda shugaban kasa ya bayar ya kuma umurci Ofishin Kamfanonin Gwamnati da ya kafa sabuwar tawagar gudanarwa ta AEDC."

Hakazalika, gwamnati ta umarci kamfanin da ya gaggauta janye yajin aikin na kwanaki 21, tare da biyan ma'aikatan hakkokinsu, kamar yadda Leadership ta ruwaito.

Buhari ya bayyana dalilin da ya sa ya kori ministocinsa biyu

A baya kunji cewa, shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana dalilin da yasa ya sallami ministoci biyu daga cikin yan fadarsa da ya zaba a ranar 21 ga watan Agustan 2019.

Kara karanta wannan

Hukumar jami'a ta kori lakcarorinta 4 bisa karbar kudi ta bayan fage da rashin da'a

Sanarwar da kakakin shugaban kasar, Femi Adesina ya fitar ta ce bukatar 'sabon jini' ne yasa aka yi sauyin ministocin kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Legit.ng ta ruwaito cewa an sallami Muhammad Sabo Nanono, Ministan Noma da Raya Karkara da Sale Mamman, Ministan Makamashi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel