Yadda Jonathan ya tilastawa Dangote da sauran kamfanoni rage kudin buhun siminti a 2014

Yadda Jonathan ya tilastawa Dangote da sauran kamfanoni rage kudin buhun siminti a 2014

  • A shekarar 2011 ne Shugaban kasa Dr. Goodluck Jonathan ya sa aka sauke farashin buhun siminti
  • Goodluck Jonathan ya ji koke-koken da Bayin Allah suke yi a kan tsadar siminti a wancan lokaci
  • Hakan ta sa ya zauna da manyan kamfanoni, ya umarce su da su rage kudi, a karshe an samu sauki

Abuja - A dalilin kukan da mutane suke yi a kan tsadar siminti a Najeriya, Dr. Goodluck Jonathan wanda shi ne shugaban kasa a 2011 ya dauki mataki.

Shugaba Goodluck Jonathan ya kira shugaban kamfanin Dangote Group da sauran masu hada siminti, ya bukaci su rage farashin buhunsu a Najeriya.

Kamar yadda sanarwa ta fito daga fadar shugaban kasa a lokacin, Mai girma Jonathan ya ba wadannan kamfanoni tsawon wata daya su karya farashi.

A wani rahoto da jaridar Vanguard ta fitar a watan Mayun 2011, an ci ma matsaya cewa akwai bukatar ayi wani abu a game da yadda siminti ya tashi.

Kara karanta wannan

Tsohon ma'aikaci ya dauki hayar Lauya, yana neman Dangote ya biya shi N50m a kotu

Kakakin shugaban kasa, Ima Niboro yace an yi zaman ne da manyan kamfanonin siminti biyar.

Buhun siminti a 2014
Buhunan siminti a Najeriya Hoto: nairametrics.com
Asali: UGC

Wadanda aka yi zama da su a taron

Wadanda aka yi wannan taro da su a wancan lokaci sun hada da shugaban kungiyar masu harkar siminti na kasa, Joseph Makoju da Alhaji Aliko Dangote.

Sai kuma shugaban BUA, Abdulsamad Rabiu da Jean-Christophe Barbant na kamfanin Lafarge Cement.

Bayan ‘yan watanni sai aka ji sanarwa daga bakin babban darektan kamfanin simintin Dangote, Devakumar Edwin yana cewa sun rage farashin kayansu.

Mista Devakumar Edwin yace buhun simintinsu mai ajin 32.5 mai cin kilogram 50 ya koma N1, 000, sannan buhun mai ajin 42.5 ya koma N1, 150 a kasuwa.

Matakin da shugaban kasan ya dauka ya jawo aka samu ragin kusan 40% a farashin kowane buhu. An yi wannan ne domin a samu saukin gina gidaje.

Kara karanta wannan

Hankula sun tashi yayin da buhun siminti ya kai N4,600 a Najeriya

Dangote ya kara arziki a 2021

A makon nan aka ji Aliko Dangote yana cigaba da hawa jerin matattakalar attajiran duniya. Ana maganar attajiran Najeriyan ya fi kasashe 30 arziki a Afirka.

Masana tattalin arziki su na ganin cewa kamfanin simintin Dangote ya samu kazamar riba a shekarar nan ne a dalilin amfani da siminti wajen yin tituna.

Asali: Legit.ng

Online view pixel