Tsohon ma'aikaci ya dauki hayar Lauya, yana neman Dangote ya biya shi N50m a kotu

Tsohon ma'aikaci ya dauki hayar Lauya, yana neman Dangote ya biya shi N50m a kotu

Anas Ibrahim ya kai karar kamfanin simintin Aliko Dangote a kotun ma’aikata na reshen jihar Kano

Wannan Bawan Allah wanda direba ne, yace an kore shi daga aiki bayan ya yi hadari ya na kan aiki

Lauyan da ya tsayawa direban ya bukaci kamfanin ya biya su N50m saboda an ki kula da lafiyarsa

Kano - Wani direba da ya yi aiki da kamfanin simintin Dangote, Anas Ibrahim ya shigar da kara a gaban kotun ma’aikata, ya na karar wadanda ya yi wa aiki.

Jaridar Daily Nigerian ta ce Anas Ibrahim ya kai kamfanin kotun NIC na reshen jihar Kano, ya na kalubalantar yadda aka kore shi daga aiki bayan ya yi hadari.

Malam Ibrahim yace an raba shi da hanyar samun abincin shi bayan ya yi hadari a hanyar Legas – Abeokuta a yayin da yake tukar motar kamfanin simintin.

Kara karanta wannan

Wani mutum ya kashe mai sayar da sigari da duka saboda N50 kacal

Lauyan da ya tsayawa wannan direba, Abba Hikima ya shaidawa kotu cewa Ibrahim ya aukawa wata mota a watan Yuli bayan ya sauke siminti a kamfani.

Daga nan direban ya fita daga hayyacinsa, sai aka sheka da shi zuwa wani babban asibitin Sango Otta, daga nan aka kai shi cibiyar FM da ke garin Abeokuta.

Tsohon ma'aikaci
Direban Dangote Hoto: dailynigerian.com
Asali: UGC

Rahoton yace wannan Direban ta bakin lauyan na sa, ya shaidawa Alkali cewa jinya ta kai shi asibitin kwararru na Sir Mohammed Sunusi da ke garin Kano.

Hikima yake cewa wannan Bawan Allah ya samu rauni uku a kugu, sannan ya yi mummunar gocewa a tafukansa, bayan wasu raunukan da ya ji a jikinsa.

Tun da abin ya faru a 2020, Hikima yace aka daina biyan direban motar albashinsa, aka kyale shi ya rika fama da dawainiyar kansaa asibitoci dabam-dabam.

Kara karanta wannan

Matashin Fasto ya yi garkuwa da babban Bishop na Katolika a jihar Imo

Hakan ta sa ya bukaci a biya shi Naira miliyan 50 a sakamakon raunin da ya yi, da Naira miliyan na ci masa zarafi, sai kuma Naira miliyan daya na aikin lauya.

Bayan ya saurari karar, Alkali mai shari’a E.D. Esele ya dakatar da shari’ar zuwa wani lokaci.

Siminti ya tashi

A wani rahoto da muka fitar, kun ji cewa hauhawar farashin kaya a Najeriya ya janyo kusan komai ya kara tsada a fadin kasar nan har da kayan gine-gine.

Siminti ya na cikin kayan da suka yi mummunar tsada a karshen shekarar nan. Wannan ya sa aka ji majalisa ta na cewa a ba kamfanoni lasisin harkar siminti.

Asali: Legit.ng

Online view pixel