Kasar Koriya za ta kashe Naira Biliyan 5 wajen magance matsalar wuta a kauyuka

Kasar Koriya za ta kashe Naira Biliyan 5 wajen magance matsalar wuta a kauyuka

  • Gwamnatin Koriya za ta samar da wutar lantarki a wasu kauyuka daga karfin hasken rana a Najeriya
  • Wannan aiki da cibiyar bunkasa fasahar zamani na kasar Koriya za tayi, zai ci fam Dala miliyan 12
  • Wani jami'i ya bada wannan sanarwa a madadin Korean Institute for Advancement of Technology

Abuja - A ranar Litinin, 6 ga watan Disamba, 2021, gwamnatin kasar Koriya ta yi alkawarin samar da kayan aikin ‘Solar’ a wasu kauyuka da ke Najeriya.

Jaridar Daily Trust ta fitar da rahoto cewa gwamnatin Koriya za ta kashe Dala miliyan 12.4 wajen aikin samar da wuta daga hasken rana a wasu wuraren.

Mataimakin shugaban cibiyar bunkasa fasaha ta koriya watau Korean Institute for Advancement of Technology, Mista Kim Jeong-Wook ya bayyana haka.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: Gwamnatin Jihar Kano ta bi dare ta sake rufe ofishin lauyan Shekarau

Kim Jeong-Wook ya yi wannan jawabi ne da yake magana a farkon makon nan a garin Abuja.

Kamar yadda rahoton ya bayyana, Jeong-Wook yace wannan aiki zai taimaka wajen samar da wuta kamar yadda suka yi niyyar taimakawa gwamnati.

Matsalar wuta a kauyuka
Kayan aikin 'Solar' Hoto: www.investopedia.com
Asali: UGC

Yadda aikin zai taimakawa 'Yan Najeriya

Cibiyar ta Korean Institute for Advancement of Technology, ta na ganin cewa aikin zai taimakawa tattalin arzikin Najeriya ta hanyar samar da ayyukan yi.

Har ila yau, Jeong-Wook yace samun wutan da za ayi aiki zai zaburar da tattalin arziki, sannan ya magance matsalar talauci, kuma ya inganta rayuwar mutane.

Korean Institute for Advancement of Technology

Legit.ng Hausa ta fahimci cewa an kafa cibiyar ne tun a shekarar 2009 a karkashin ma’aikatar tattalin arziki na ilmi domin a kawo cigaban fasaha a Duniya.

Kara karanta wannan

EFCC ta cigaba da gabatar da hujjoji a kotu da za su sa a daure tsohon gwamna Fayose

Korea Institute for Advancement of Technology tayi suna wajen bincike da kirkire-kirkire na fasahan zamani da za su taimakawa Koriya da sauran kasashe.

Shekaru sama da 60 da samun ‘yancin-kai, har yau ana fama da matsalar wutar lantarki a Najeriya.

Direban Dangote ya kai kamfani kotu

A shekarar 2020 ne kamfanin Dangote ya kori wani Direbansa da ya yi rugu-rugu a sakamakon hadari da ya samu wajen tukar motar kamfanin siminti a Legas.

Wannan mutumi ya nemi lauya, ya shigar da kara a kotu a kotu, ya na neman a biya shi miliyoyin kudi saboda watsi da shi da kamfani ya yi bayan ya samu larura.

Asali: Legit.ng

Online view pixel