An kawo sabon tsari, kowane Likita zai biya N900, 000 kafin samun lasisin aiki a asibiti - MDCN

An kawo sabon tsari, kowane Likita zai biya N900, 000 kafin samun lasisin aiki a asibiti - MDCN

  • Majalisar MDCN mai kula da aikin likitoci a Najeriya ta tsawaita wa’adin horas da daliban ketare
  • A wata sanarwa da MDCN ta fitar, ta ce za a rika horar da wanda ya yi karatu a waje na wata shida
  • Dalibai masu niyyar yin jarrabawar samun lasisin aiki a asibitocin Najeriya za su biya N900, 000

A ranar 1 ga watan Disamba, 2021, majalisar MDCN mai kula da likitoci a Najeriya ta kawo wani sabon tsarin horas da likitocin da suka yi karatu a ketare.

The Cable ta fitar da rahoto a ranar Laraba, inda aka ji duk dalibin da ya karanci ilmin likitanci a kasashen waje, zai samu karin horo idan ya dawo Najeriya.

Majalisar ta MDCN tace ‘yan Najeriya za su biya N900, 000 domin a ba su wannan horo, yayin da wadanda ba ‘yan kasa ba kuma za su biya N1, 400, 000.00.

Kara karanta wannan

Akwai yiwuwar Kotu ta sake sakin jagoran kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu a zaman shari’ar yau

Za a dauki watanni shida ana horas da wadannan rukuni na dalibai da suka yi karatu a ketare. MDCN tace idan aka biya wadannan kudi ba za su dawo ba.

Yadda tsarin zai yi aiki

Wannan tsari zai fara aiki a shekara mai zuwa kamar yadda sanarwar da aka fitar a shafin MDCN ta nuna.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sahun farko na wadanda za a horas za su fara wannan kwas ne a Junairun 2022, za a kammala a watan Yuni. Bayan nan ne sai su yi jarrabawar samun lasisi.

MDCN tace an zabi asibitocin koyon aiki a kowane yanki da za ayi amfani da su wajen bada horon. Daga ciki akwai asibiti na jami’ar Olabisi Onabanjo.

Sauran sun hada da; Asibitin koyon aiki na jami’ar jihar Enugu, na jami’ar Fatakwal, jami’ar Ilorin, jami’ar Maiduguri ta UNIMAID da asibitin Malam Aminu Kano.

Kara karanta wannan

Litar man fetur zai zarce N340 a farkon shekarar 2022 idan gwamnati ta cire tallafi - ‘Yan kasuwa

Asibiti
Likitoci a asibiti Hoto: www.theweek.in
Asali: UGC

“MDCN ta na sanar da duk daliban da aka horar a kasashen waje cewa daga Disamban 2021, masu niyyar yin jarrabawar samun lasisi, za su yi kwas na tsawon watanni shida, kafin su iya rubuta jarrabawar sharer fagen MDCN.” – Hukumar MDCN.
“Rukunin farko za su fara ne a watan Junairu, su kammala a watan Yunin 2022. Za a sa ranar sauran da za a yi bayan nan, a tallata kamar yadda ya kamata.”

Martanin wasu likitoci

Legit.ng Hausa ta nemi jin ta bakin wasu likitoci da ke aiki a Najeriya, a game da wannan doka.

"Alal hakika wannan ba sabon abu ba ne, an yi shekaru ana yin wannan. Nima na shiga wannan tsari. A shekarun baya sai aka soke shi, na gagara gane dalilin yin hakan.
A kan yi watanni uku ne ana horas da wadanda suka karanci liktanci a kasashen waje. Ana samun wuri na musamman, ayi masu bita domin su shiryawa jarrabawar samun lasisi.

Kara karanta wannan

Ayyuka 257 aka kwafo daga kasafin kudin 2021 masu darajar N20bn, ICPC

Matsalar dai kurum ita ce kudin, N900, 000 ya yi yawa. Amma watanni shida sun yi."

- Dr. Kabir Salisu, wani likita da yake aiki a Katsina.

Dr. Shamsuddeen Nasir, wani likitan lafiyar kwakwalwa ya shaida mana cewa wa’adin biyan kudin ya yi kadan, sannan asibitocin da aka zaba ba su da yawa.

“Ina da matsala da kudin da aka sa, kusan N1m, ya yi yawa ga musamman iyayen da ba su da hali, gwamnati ce ta dauki nauyin karatun ‘ya ‘yansu.”
“Amma idan ka duba kudin karatun, kusan N150, 000 kenan duk wata, idan ka yi la’akari da kwararrun da za a dauko, kudin bai yi wani yawa ba.”
“Duk da haka dai ya fi karfin talaka, MDCN su duba wannan. Ina bada shawarar bada damar biyan kudin gutsin-gutsin.” – Dr. Shamsuddeen Nasir.

Dr. Siddiqa Sallau ta bayyana mana cewa idan aka duba abin ta bangaren tattali, kudin da aka sa sun yi yawa.

Kara karanta wannan

Yan bindiga da Sojojin sun yi musayar wuta a Imo kan umarnin zama a gida na IPOB

N900, 000 sun yi yawa!

Wannan kamar cewa ba a son likitoci ne a Najeriya. Wadanda mu ke da su, su na tserewa. A kullum abubuwa su na kara yi wa Likitoci wahala a Nejeriya, a cewar likitar.

Amma ta ce ya na da kyau a horas da likitocin da suka yi karatu a ketare, kuma wannan ba yau aka fara ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel