Yadda dukiyar Dangote ta kara yawa a 2021 fiye da ninkin yadda ya mallaka a baya

Yadda dukiyar Dangote ta kara yawa a 2021 fiye da ninkin yadda ya mallaka a baya

  • A karo na goma sha daya a jere, Aliko Dangote na shirin fitowa a shekarar nan a matsayin wanda ya fi kowa kudi a Afrika
  • A cikin 2021 zai iya yin hakan tare da tsallake yadda ya zarce matakin da ya taba hawa a cikin shekaru bakwai da suka gabata
  • Bangarorin Dangote sun hada da gishiri, fulawa, da sukari, da dai sauransu, amma yawancin arzikinsa zai fito ne daga kamfanin simintinsa a bana

Attajirin da ya fi kowa kudi a Afirka, Aliko Dangote, yana kan ganiyar sake lashe wannan mataki a shekarar, matsayin da ya lashe tun a shekarar 2014 wanda kuma zai zarce a karo na biyu a jere a sashinsa na siminti.

Tashin farashin hannun jarin kamfanin simintin Dangote da na man fetur da taki sun taimaka wajen bunkasa arzikinsa da ya kai dala biliyan 2.3 a bana zuwa dala biliyan 20.1 a ranar 3 ga watan Disamba, wanda ya kasance mafi arziki tun 2014, inji Bloomberg Bilionaires Index.

Kara karanta wannan

'Yan crypto sun tafka mummunar asara yayin da darajar Bitcoin ta dungura kasa

Mai kudin Afrika, Aliko Dangote
Yadda dukiyar Dangote ta kara yawa a 2021 fiye da ninkin yadda ya mallaka a baya | Hoto: nairametrics.com
Asali: UGC

Daga ina kudin Dangote suke fitowa?

A cewar Bloomberg, tsananin bukatar siminti da hauhawar farashin kayayyakin gine-gine a Najeriya, sun taimaka wajen habaka kudaden shiga na kamfanin Simintin Dangote.

Kamfanin simintin Dangote shi ne babban kadaran da ya fi kowanne daraja a kayayyakin attajirin.

Tun daga farkon shekarar 2021, darajar hannun jarin kamfanin simintin Dangote ya karu da 24.49% daga N224.90 kan kowane kaso a ranar Litinin 4 ga watan Janairu zuwa N280 zuwa a ranar Juma’a 3 ga Disamba, 2021.

Simintin Dangote ba wai kamfani ne kawai mafi daraja a harkar hada-hadar Najeriya ba, yana daya daga cikin manyan masu daukar ma'aikata a kasar.

Sauran hanyoyin samun arzikinsa

Bloomberg ya kuma lura cewa Dangote ya kuma shirya kammala wani aikin matatar mai da ta kai dalar Amurka biliyan 19 wacce za ta iya biyan fiye bukatar man fetur a Najeriya.

Kara karanta wannan

Lokacin mu ne: ‘Dalibin Jami'a mai shekara 28 zai yi takarar Shugaban matasa a Jam’iyyar APC

Dangote, a bana, ya kuma fara fitar da taki zuwa kasashen Amurka da Brazil bayan kammala wani katafaren kamfanin da zai iya samar da ton miliyan 3 na nau'in takin urea da ammonia a duk shekara.

'Yan crypto sun tafka mummunar asara yayin da darajar Bitcoin ta dungura kasa

A wani labarin, 'yan crypto sun tafka babban faduwa a ranar Asabar bayan Bitcoin da wasu tsabobin intanet suka rage darajar sama da dala biliyan daya.

Wannan na faruwa ne yayin da 'yan crypto a duniya suka sayar da tsabobin kudaden intanet don daidaituwa da amintattun hannayen jari yayin da bukukuwan Kirsimeti ke gabatowa.

Bitcoin shine mafi daraja a tsabobin kudaden intanet a daraja ta kasuwa, ya fado da 31.6% daga darajar $69,000 mafi girma a shekarar nan a ranar 10 ga Nuwamba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel