Annobar Korona ta kawo min cikas wajen yaki da rashawa, Buhari ga Shugabannin duniya a Dubai

Annobar Korona ta kawo min cikas wajen yaki da rashawa, Buhari ga Shugabannin duniya a Dubai

  • Shugaba Muhammadu Buhari ya halarci taron baja kolin EXPO 2020 dake gudana yanzu haka a birnin Dubai
  • Shugaban kasan wanda ya halarci 'Ranar Najeriya' a taron yayi jawabin irin nasarorin da gwamnatinsa ta samu
  • Buhari ya bayyana yadda annobar Korona ta kawo masa cikas wajen yaki da cin hanci da rashawa

Birnin Dubai - Shugaba Muhammadu Buhari ya yi kira ga Shugabannin Duniya su hada karfi da karfe wajen fuskantar kalubalen da al'ummar duniya ke fuskanta.

A jawabin da ya gabatar ranar Juma'a, 3 ga Disamba, yayin taro EXPO 2020 dake gudana a Dubai, Shugaban Najeriyan ya bayyana cewa hada kai zai taimaka wajen kawar da annobar Korona a fadin duniya.

A jawabin da mai magana da yawunsa, Femi Adesina, ya saki a shafinsa na Facebook, Shugaba Buhari ya bayyana yadda Annobar Korona ta janyowa tattalin arzikin Najeriya koma baya da kuma yaki da rashawa.

Kara karanta wannan

Mataimakin Shugaban kasa ya bayyana abin da zai faru idan aka yi gigin barka Najeriya

Adesina yace:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Shugaba Buhari ya bayyanawa EXPO cewa Najeriya, kamar sauran kasashen duniya sun illaltu da annobar COVID-19, wanda ya tsananta lamarin tsaro, yaki da rashawa da kuma fadada tattalin arzikin kasar."
"Amma duk da haka, ya bayyana cewa gwamnatinsa ta samu nasarori cikin kankanin lokaci."

Buhari ga Shugabannin duniya a Dubai
Annobar Korona ta kawo min cikas wajen yaki da rashawa, Buhari ga Shugabannin duniya a Dubai Hoto: Femi Adesina
Asali: Facebook

Buhari ya godewa Shugaban kasar UAE

Shugaban kasan ya mika godiyarsa ga mika godiyarsa ga Shugaban kasar UAE, Sheikh Khalifa Bin Zayed Al Nahyan, bisa gayyatarsa wannan taro kuma da ya samu halartan 'ranar baja kolin Najeriya.'

Buhari yace wannan dama ya baiwa Najeriya daman nunawa duniya itace kasa a nahiyar Afrika mafi girman tattalin arziki.

Shugaba Muhammadu Buhari ya dira birnin Dubai

Shugaba Muhammadu Buhari ya dira birnin Dubai, haddadiyar daular Larabawa da daren Laraba domin halartan taron baja kolin EXPO 2020.

Kara karanta wannan

An gano abin da Buhari ya fadawa Shugaban kasar Afrika ta Kudu kafin ya lula zuwa Dubai

Hadimin shugaban kasa, Buhari Sallau, ya bayyana hakan a jawabin da ya saki kuma Legit ta samu.

Shugaban zai samu rakiyar ministoci da jami'an gwamnati sama da 10.

Asali: Legit.ng

Online view pixel