Hukumar jiragen sama ta musanta rahotannin tashin bam a filin jirgin Maiduguri

Hukumar jiragen sama ta musanta rahotannin tashin bam a filin jirgin Maiduguri

  • Hukumar kula da filayen jiragen sama ta Najeriya ta karyata rahotannin tashin bam a filin jirgin Maiduguri
  • A jiya ne aka samu rahotanni da ke cewa, an samu fashewar bam a wani yankin filin jirgin saman Maiduguri
  • Hukumar ta yi bayani, tare da bayyana gaskiyar lamarin inda tace babu ta yadda aka samu wani a hari a filin

Borno - Hukumar kula da filayen tashi da saukar jiragen sama ta Najeriya (FAAN) ta musanta rahotannin tashin bam a filin jirgin Maiduguri.

Wata sanarwa a ranar Asabar da kakakin FAAN, Henrietta Yakubu ya fitar, ta ce:

"Ba a kai wa filin jirgin saman hari ba, kuma ba a kai hari ko wanne bangarensa ba."
Taswirar jihar Borno
Hukumar jiragen sama ta musanta rahotannin tashin bam a filin jirgin Maiduguri | Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Sanarwar ta kara da cewa:

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kano ta bayyana dalilin ta na garkame ofishin lauyan Shekarau

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Game da rahoton da aka samu ta yanar gizo da ke cewa bam ya tashi a filin jirgi na Maiduguri da ake zargin mayakan Boko Haram ne suka shirya, hukumar ta FAAN ta sanar da fasinjoji da sauran jama'a cewa babu wani fashewa, ko kutse a filin jirgin Maiduguri."

Tashar talabijin ta Channels ta rawaito cewa an samu fashewar wani abu da sanyin safiyar Asabar a wani gida da ke Maiduguri babban birnin jihar Borno.

Rahoton na Channels ya ce gidan yana kan hanyar Maiduguri zuwa Damaturu.

Rahoton ya kara da cewa fashewar ta afku a kasa da mita 100 da wani sansanin tubabbun ‘yan Boko Haram, inda gidaje kusan 12 suka lalace.

A Maiduguri dai an samu raguwar hare-haren 'yan tada kayar baya a 'yan kwanakin nan.

Kara karanta wannan

Bayan shafe fiye da wata 6 cikin duhu, Zulum ya sanar da ranar da za dawo da lantarki a Maiduguri

Akalla mutane 10 ne suka mutu sannan kusan 60 suka jikkata bayan da mayakan Boko Haram suka kai hari garin a watan Fabrairu, Premium Times ta rahoto.

Tara daga cikin wadanda suka mutu wasu kananan yara ne da bam ya tashi dasu a lokacin da suke wasan kwallon kafa.

Mutane sun jikkata, yayinda ake harba manyan rokoki cikin garin Maiduguri

A wani bangaren, mazaunan rukunin gidajen 1000 Housing Estate dake cikin Maiduguri sun waye gari ranar Asabar da tashin bama-bamai.

Vanguard ta ruwaito cewa akalla karar bama-bamai hudu aka ji cikin gundumar Gomari da 1000 Housing Estate.

Ana kyautata zaton cewa yan ta'addan Boko Haram suka kai wannan hari ta hanyar harba rokoki cikin gari yayinda Sojoji ke kokarin kawar da su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel