Bayan shafe fiye da wata 6 cikin duhu, Zulum ya sanar da ranar da za a dawo da lantarki a Maiduguri

Bayan shafe fiye da wata 6 cikin duhu, Zulum ya sanar da ranar da za a dawo da lantarki a Maiduguri

  • Farfesa Babagana Zulum, gwamnan jihar Borno ya ce nan da kwanaki 30 za a gyara lantarki a Maiduguri
  • Gwamna Zulum ya bayyana hakan ne yayin da ya ke gabatar da kudirin daidaita kasafin kudi na shekarar 2022 a Majalisar Jihar
  • An shafe kimanin shekara guda babu wutan lantarki a Maiduguri tun bayan da yan ta'adda suka lalata layukan lantarkin

Jihar Borno - Gwamna Jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum na jihar Borno ya bada tabbacin cewa za a dawo da wutar lantarki a Maiduguri da kewaye cikin kwanaki 30, Daily Trust ta ruwaito.

Babban birnin jihar ta Borno ta kasance cikin duhu tun lokacin da 'yan ta'adda suka lalata layukan lantarkin garin da ke hanyar Maidugri zuwa Damaturu watanni 11 da suka gabata.

Bayan shafe fiye da wata 6 cikin duhu, Zulum ya sanar da ranar da za dawo da lantarki a Maiduguri
Gwamnan Borno, Babagana Zulum. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

Kara karanta wannan

Da izinin Allah zamu dawo da wutar Lantarki Maiduguri cikin kwana 30, Gwamna Zulum

Yayin da ya ke gabatar da kasafin kudi ta shekarar 2022 a gaban majalisar jihar, a ranar Talata, gwamnan ya ce ana kokarin dawo da lantarki a garin kamar yadda ya zo a ruwayar ta Daily Trust.

A cewarsa:

"Insha Allah, za mu cigaba da zage damtse domin ganin an dawo da lantarki a Maiduguri da kewaye cikin kwanaki 30.
"Kamar yadda dukkan ku kuka sani babu wuta a babban birnin jihar kusan shekara guda. Ba za mu yi kasa a gwiwa ba a bangaren mu."

Gwamnatin jihar ta Borno, a lokuta da dama, ta yi kokarin gyara wutan lantarkin ta hanyar biyan kudin gyaran amma yan ta'addan suna ta yi mata zagon kasa.

Rashin wutan yana cigaba da shafan yan kasuwa, mutanen gari da wasu hukumomin gwamnatin jihar da suke dogara kan layukan lantarkn zalla don ayyukansu.

Kara karanta wannan

Shirin kidaya yawan yan Najeriya zai lakume sama da Biliyan N190bn a 2022, Majalisa

'Yan sanda sun hana 'yan ta'addan Boko Haram sace soja da fasinjoji 15 a Borno

A wani labarin, jami'an yan sanda sun hana wasu da ake zargin yan Boko Haram ne sace wani jami'in soja a jihar Borno, majiyoyi suka shaidawa The Cable.

Sojan, wanda ke aiki a bataliyar sojoji da ke Marte, yana kan hanyarsa daga Damaturu zuwa Maiduguri ne lokacin da yan ta'addan suka kai hari.

Majiyoyi sun ce yan sandan sun kuma hana yan ta'addan sace wasu fasinjoji guda 15, The Cable ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel