Da duminsa: Mutane sun jikkata, yayinda ake harba manyan rokoki cikin garin Maiduguri

Da duminsa: Mutane sun jikkata, yayinda ake harba manyan rokoki cikin garin Maiduguri

  • Al'ummar Maiduguri a ranar Asabar sun wae gari da hare-hare har cikin dakunansu
  • Yan ta'addan ISWAP ake zargin suna harba rokoki cikin gidajen mutane da sanyin safiya
  • Kawo yanzu ba'a rashin rai ba amma wasu mutane sun samu kananan raunuka

Maiduguri, jihar Borno - Mazaunan rukunin gidajen 1000 Housing Estate dake cikin Maiduguri sun waye gari ranar Asabar da tashin bama-bamai.

Vanguard ta ruwaito cewa akalla karar bama-bamai hudu aka ji cikin gundumar Gomari da 1000 Housing Estate.

Ana kyautata zaton cewa yan ta'addan Boko Haram suka kai wannan hari ta hanyar harba rokoki cikin gari yayinda Sojoji ke kokarin kawar da su.

A cewar wani mai idon shaida, bama-bamai biyu sun fara tashi ne a tashar jirgin sama dake Gomari.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Kotun daukaka kara ta sako faston da aka yanke wa hukuncin daurin rai da rai

Bama-bamai ke tashi cikin garin Maiduguri
Da duminsa: Mutane sun jikkata, yayinda bama-bamai ke tashi cikin garin Maiduguri Hoto: Vanguard
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Na godewa Allah, mutumin da ya tsallake rijiya da baya

Wani mutumi da ya tsallake rijiya da baya bayan roka ya dira cikin gidansa, Mallam Kulima, ya mika godiyarsa ga Allah bisa kare rayuwarsa da na iyalansa.

Yace:

"Yau ranar bakin ciki ce a 1000 Housing Estate, Borno, saboda Roka ta dira cikin gidana dake 2589, Elkenemi street."
"Ina cikin daki lokacin da rokar ta dira dakin uwargidata."
"Wasu daga cikin iyalina sun samu raunuka iri-rir kuma an garzaya da su asibiti."

Wani mazauni mai suna Usman Ali yace:

"Tashin bam din ya lalata wani gida dake kusa da gidana, bai kashe kowa ba amma wani karamin karamin yaro dan shekara 9 ya ji rauni."

Wani mai idon shaida, Usman Zanna Gomari yace:

"Muna zargin yan Boko Haram ne suka harba kuma muna tunanin suna son kai hari masaukin maniyyata aikin Hajji (Hajj Camp) inda aka ajiye tubabbun yan Boko Haram."

Kara karanta wannan

Da duminsa: Yan bindiga kai hari Kaduna, sun kashe 2, sun sace 50

"Ka san mun dade muna korafi kan cigaba da ajiye tubabbun yan ta'addan cikin gari. Idan ka lura, sun dade suna kai hare-haren unguwannin da aka ajiye tsaffin abokansu."

Asali: Legit.ng

Online view pixel