Amfanin Na’a-Na’a a jikin dan Adam

Amfanin Na’a-Na’a a jikin dan Adam

Na’a-na’a wata shuka ce mai albarka wadda ta shahara a nahiyar Turai, Afirka, Asia, Australia, da kuma Amurka ta Arewa, inda ake amfani da ita a matsayin kayan kamshi da kuma maganin gargajiya musamman a cikin shayi.

Ganyen na’a-na’a kore ne mai dadin kamshi da ke sanyaya rai ga duk wanda ya shake shi. Na’a-na’a na da sinadarin ‘minti’ (wato ‘menthol’) mai sanyaya rai da kuma inganta lafiyar dan Adam.

Ana amfani da na’a-na’a wajen sarrafa wasu kayan amfanin gida da muke siya na yau da kullum, wato kayan amfani da muke siya a kasuwa kamar irinsu man goge hakori, sabulai, man-shafawa, alawowi, sinadarin kurkura da tsaftace baki, magungunan shafawa, da sauran su.

Bincike ya nuna cewa, shukar na’a-na’a wadda ta fito daga dangin ciyayi ake kira mentha ta samo asali ne ta hanyar auren-shuka, Hybridization a Turance, wato auren shuka mai suna ‘watermint’ da kuma wata shukar mai suna ‘spearmint’.

Haka kuma bincike ya nuna cewa na’a-na’a ta zo ne daga kasashen Turawa da Larabawa. Inda al'ummar wannan yankuna ke amfani da ganyen na’a-na’a cikin abinci da kuma a matsayin ganyen-shayi.

KARANTA KUMA: Sirrika 10 na ganyen gwaiba wajen bunkasa lafiyar bil Adama

Ana kuma samun man na’a-na’a da ruwanta a kasuwanni domin alfanu daban-daban. Bincike ya nuna cewa na’a-na’a na da amfani da yawa ga lafiyar dan’adam. Ana sarrafa ta hanyoyim daban-daban domin cin moriyarta

Ga wasu daga cikin alfanin na'a-na'a ga rayuwar dan Adam:

1. Tana magance matsalar ciwon ciki da rashin fitar bahaya cikin sauki. Ana hada shayin na’a-na’a ko a zuba manta cikin shayi marar madara sai a sha.

2. Tana saukaka narkewar abinci. Ta kan taimaka wajen narkar da abinci yadda sassan jiki za su yi amfani da shi.

3. Tana maganin dukkanin wata dangin cuta ta sanyi ko mura. Ana amfani da man na’a-na’a ko ganyen a tafasa cikin shayi marar madara, haka kuma, za a iya amfani da man na’a-na’a cikin ruwan zafi, a yi turiri, a lullube da mayafi wato sirace a Hausance.

4. Maganin ciwon kai. Ana shafa man na'a-na'a a bangaren da kai ke ciwo.

5. Maganin ciwon jiki. Ana shafa manta ga jijiyoyi ko sassan jiki dake ciwo.

6. Maganin ciwon hakori. Ana yi amfani da man na’a-na’a da auduga inda ake diga man ga auduga sa’annan a manna ga hakori da ke ciwo.

7. Ana iya shafa manta a bangaren jiki da ke kaikayi domin samun sauki.

8. Korar sauro. Ana shafa man na’a-na’a a jiki domin kamshinta kadai yana korar sauro.

9. Na'a-na'a ta na kashe tsutsar ciki.

10. Tana bunkasa lafiyar hanta wajen dukkanin gudanarwarta

11. Na'a-na'a tana hana damuwa a yayin da aka tafasa ganyen ta cikin shayi, ko kuma a zuba manta a cikin kofin shayi safe da yamma.

12. Tana kara kaifin basira wajen taimakawa kwakwalwa rike karatu da fahimta. Ana hada shayi da ganyen na’a-na’a a rinka sha da zuma.

13. Tana sanya girki yayi kamshin a matsayin sunadarin kamshi. Ana yin amfani da ganyen wajen girki domin kuwa hakan ya kan taimaka wajen son cin abinci musamman ga wanda sha'awar abinci ta fita daga ransa.

14. Tana maganin ciwon ciki musamman ga mata masu matsalolin al’ada.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel