Mai gadi ya kira ruwa: Ya fita shakatawa da motar maigidansa ba tare da saninsa ba

Mai gadi ya kira ruwa: Ya fita shakatawa da motar maigidansa ba tare da saninsa ba

  • Wani mai gadi ya kira kansa ruwa yayinda ya buge gini da motar maigidansa cikin gidan makwabta
  • An ruwaito cewa mai gadin ya dauki motar ne ba tare da sanin maigidansa ba lokacin da abin ya faru
  • Bayan lalata motar da yayi, masu gidan da ya buge katangarsu sun lashi takobin cewa sai ya biya

Wani maigadi ya shiga uku sau uku yayinda yayi mumunan hadari da mota maigidansa.

Mai gadin wanda ba'a bayyana sunansa ba ya dauki motar ne ba tare da sanin maigidansa ba kafin shiga cikin gini.

A bidiyon da Instablog9ja ta daura a shafin IG, wanda ya nadi abin da ya faru ya bayyana cewa yanzu masu gidajen da ya buge sun fara rikici.

Kara karanta wannan

BaAmurkiya mai digiri 4 ta gangaro Afrika, ta yi wuff da dan achaba, tace hadin Ubangiji ne

Mai gadi ya kira ruwa
Mai gadi ya kira ruwa: Ya fita shakatawa da motar maigidansa ba tare da saninsa ba Hoto: Instablog9ja
Asali: Instagram

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Mai gidan da motar tayi rami ya ce mai daya gidan sai ya gyara masa katangarsa.

Amma mai gidan ya bayyana cewa mai motan bai gidan yake zama ba kuma basu san shi ba, saboda haka ba su zasu biya ba.

An tafi da mai gadin da ya kira ruwan ofishin yan sanda lokacin da aka nadi bidiyon.

Kalli bidiyon:

Yan Najeriya sun yi tsokaci

Muhammad Daha Abdullahi yace:

Duk Tsuntsun da Ya ja Ruwa.....Shi Ruwa kan Doka

Yusuf Amowa Waja yace:

Sai hakuri dafatan Allah kiyaye nagaba aikin gama yagama

Habu Atafi'n Hadejia yace:

Sai ya sallami kansa ba tare da ya tsaya sallama ba

Yahuza Ibrahim Faska yace:

Toh fa!! Allah ya kyauta

Umar Yakubu Akuyam yace:

Mai gadi ahakan zaka koya next time a riqa tambaya kafin a dauki mota

Kara karanta wannan

Babbar magana: Yadda wani mutumi ya sayi mataccen gida kan kudi N416m ta yanar gizo

Kaci sa a ma gidan makwabcin babu fenti

Namai Fura Zangon Kanya yace:

son xuciya bacinta kaga yajama kansa ko?

Hamza Balarabe Alhazawa yace:

Subhanallah ALLAH yaƙara kiyayewa

Ibrahim Abdullahi

Inde yadawo lafiya ai shikenan dani yayi

Umar Adam Ishaq

Tofah lallai akwai cakwakiya

Asali: Legit.ng

Online view pixel