Nasara: Sojin Najeriya sun ragargaji 'yan ta'adda a luguden da suka musu a Buni Yadi

Nasara: Sojin Najeriya sun ragargaji 'yan ta'adda a luguden da suka musu a Buni Yadi

  • Sojojin Najeriya sun yi wa 'yan ta'adda luguden wuta inda suka halaka wasu yayin da wasu suka tsere a garin Buni Yadi da ke karamar hukumar Gujba
  • Kamar yadda rundunar ta wallafa, sojojin sun dakile yunkurin 'yan ta'addan na shiga garin Buni Yadi a kan wasu motocin yaki
  • Bayan ragargazar 'yan ta'addan da sojoji suka yi, wasu 'yan ta'addan sun sheka lahira yayin da wasu suka tsere amma sojin sun bi su

Borno - Rundunar sojin Najeriya ta Operation HADIN KAI (OPHK) da ke yankin arewa maso gabas, ta yi wa mayakan ta'addanci Boko Haram da na ISWAP luguden wuta a musayar wutan da suke yi a garin Buni Yadi da ke karamar hukumar Gujba ta jihar Yobe a ranar Talata, 30 ga watan Nuwamban 2021.

Kara karanta wannan

Ana cikin gwabzawa, Mayakan ISWAP suka tarwatse yayin da suka hangi jirgin yakin Super Tucano na shawagi

'Yan ta'addan da suka yi yunkurin shiga garin Buni yadi a motocin yaki sun hadu da zakakuran dakarun sojin da suka samu taimakon sojin sama da 'yan sanda inda suka ragargaji 'yan ta'addan.

Nasara: Sojin Najeriya sun ragargaji 'yan ta'adda a luguden da suka musu a Buni Yadi
Nasara: Sojin Najeriya sun ragargaji 'yan ta'adda a luguden da suka musu a Buni Yadi. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Kamar yadda rundunar ta wallafa a shafin ta na Facebook, gagarumin artabun ya sanya 'yan ta'addan sun tsere yayin da suka rasa mayakansu masu yawa.

Dakarun sojin Najeriya sun kama motocin yaki masu yawa tare da 'yan ta'addan da suke ciki.

Binciken farko da aka fara yi bayan kammala luguden wutan, an gano cewa saiti tare da kokarin sojin sama da na kasan ya kawo karshen 'yan ta'adda masu tarin yawa da motocin yakin su.

Har a halin yanzu, sojojin suna cigaba da bibiyar 'yan ta'addan da suka tsere domin halaka su.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun hana 'yan ta'addan Boko Haram sace soja da fasinjoji 15 a Borno

A yayin jinjina wa dakarun sojin, shugaban sojin kasa, Laftanal Janar Faruk Yahaya ya yi kira gare su da cigaba da hana 'yan ta'addan sakat.

Jami'an JTF sun damke dan Boko Haram, sun sheke 3 kan hanyar Maiduguri-Damaturu

A wani labari na daban, jami’an tsaron hadin guiwa, CJTF, wata kungiyar ‘yan sa kai masu taya sojoji ayyuka a arewa maso gabas, sun kama wani dan ta’adda sannan sun halaka 3 suna tsaka da satar kayan abinci a gona dake kan titin Maiduguri zuwa Damaturu.

PRNigeria ta tattara bayanai akan yadda ‘yan sa kan suka yi wa ‘yan ta’addan kwanton bauna su ka ritsa su suna sata.

Wata majiya ta sanar da PRNigeria cewa ‘yan ta’addan sun kai wa manoman farmaki a ranar Alhamis da misalin karfe 3:30pm kusa da Daiwa.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel