Jami'an JTF sun damke dan Boko Haram, sun sheke 3 kan hanyar Maiduguri-Damaturu

Jami'an JTF sun damke dan Boko Haram, sun sheke 3 kan hanyar Maiduguri-Damaturu

  • Jami’an JTF a arewa maso gabas, sun kama wani dan ta’adda da ransa sannan sun halaka 3 yayin da su ke tsaka da satar kayan abinci a titin Maiduguri zuwa Damaturu
  • Wata majiya ta bayyana yadda lamarin ya auku da misalin karfe 3:30pm kusa da Daiwa, ‘yan ta’addan sun harbi wasu manoma inda suka halaka 2 sannan suka ji wa daya rauni
  • Kwamandan rundunar, Saminu Audu ne ya jagorance su inda suka ritsa ‘yan ta’addan a Lamboa, tsakanin Mainok-Jakana suka yi musu lugude

Borno - Jami’an tsaron hadin guiwa, CJTF, wata kungiyar ‘yan sa kai masu taya sojoji ayyuka a arewa maso gabas, sun kama wani dan ta’adda sannan sun halaka 3 suna tsaka da satar kayan abinci a gona dake kan titin Maiduguri zuwa Damaturu.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: 'Yan bindiga ta'addanci kadai suke aikatawa, ba 'yan ta'adda bane, inji Gumi

PRNigeria ta tattara bayanai akan yadda ‘yan sa kan suka yi wa ‘yan ta’addan kwanton bauna su ka ritsa su suna sata.

Jami'an JTF sun damke dan Boko Haram, sun sheke 3 kan hanyar Maiduguri-Damaturu
Jami'an JTF sun damke dan Boko Haram, sun sheke 3 kan hanyar Maiduguri-Damaturu. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Wata majiya ta sanar da PRNigeria cewa ‘yan ta’addan sun kai wa manoman farmaki a ranar Alhamis da misalin karfe 3:30pm kusa da Daiwa.

Kamar yadda majiyar ta shaida:

“Yan ta’addan sun harbi manoma inda suka halaka 2 yayin da suka ji wa daya rauni.
“Sai dai kwamandan rundunar, Saminu Audu ya jagorance yaransa inda suka afka wa ‘yan bindigan a Lamboa, tsakanin Minok-Jakana kan titin Damaturu zuwa Maiduguri.
“Bayan kai musu farmakin, an halaka ‘yan ta’adda 3 sannan sun kama daya da ran shi.
“Yan ta’addan ragowar ‘yan Boko Haram na bangaren Abubakar Shekau ne wadanda suka ki hada kai da ‘yan ISWAP. Sun dogara da fashi da makamai da kuma garkuwa da mutane don samun yadda za su rayu.”

Kara karanta wannan

Zamfara: 'Yan bindiga sun tayar da wani ƙauye bayan sun yi wa mutum 7 kisar gilla

Yayin da soji suke lugude kan Boko Haram a Malam Fatori, 'yan ta'adda sun mika makamansu a Gwoza

A wani labari na daban, wasu mayakan Boko Haram sun mika wuya tare da ajiye makamansu a ranar Laraba a garin Gwoza yayin da dakarun sojin Najeriya ke tsaka da ruwan wuta a kan wasu 'yan ta'addan a Malam Fatori da yammacin Laraba.

Duk da 'yan ta'addan ISWAP sun so hana hakan, kwamandojin Boko Haram da wasu mayakansu sun mika makamansu ga sojojin.

Wata majiyar tsaro ta sanar da PRNigeria cewa, mayakan Boko haram masu yawa za su mika makamansu kafin shekarar nan ta kare.

"Wasu tsoffin kwamandojin Boko Haram da mambobinsu sun tsero daga yankin Jaje da ke dajin Sambisa kuma da kansu suka mika wuya ga sojojin rundunar Operation Hadin Kai ta bataliya ta 192 da ke kan titin Gwoza zuwa Limankara a jihar Borno."

Kara karanta wannan

Karyar takunkumi Gwamnati ke yi, Sanatoci sun gano ana daukar yaran manya aiki a boye

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel