Kotu ta ba Jami'a gaskiya, an karbe digirin da aka ba tsohon Gwamna shekaru 8 da suka wuce

Kotu ta ba Jami'a gaskiya, an karbe digirin da aka ba tsohon Gwamna shekaru 8 da suka wuce

  • Kotun daukaka kara ta rusa nasarar da Sanatan Abia, Orji Uzor Kalu ya samu a kan jami’ar ABSU
  • Alkalin babban kotun yace kotun tarayya sun yi kuskure wajen dawowa Kalu da takardar digirinsa
  • Jami’ar jihar Abia ta karbe satifiket din da ta ba tsohon gwamnan a 2013, hakan ya sa aka shiga kotu

Imo - Babban kotun daukaka kara da ke zama a garin Owerri, jihar Imo, ta ruguza hukuncin da Alkali ta yanke na maidawa Orji Uzor Kalu satifiket dinsa.

Jaridar Punch tace kotun daukaka karar ta yi zama a ranar Talata, 30 ga watan Nuwamba, 2021, inda ta zartar da hukunci a kan Sanatan Abia, Orji Uzor Kalu.

Oludotun Adefope-Okojie ta ce an yi kuskure wajen ba Orji Uzor Kalu gaskiya a kotun tarayya.

Kara karanta wannan

Rikicin Goje da Inuwa: Kotu ta tasa keyar hadimin Goje zuwa kotu saboda yin rubutu a Facebook

Gidan talabijin na Channels TV ta rahoto cewa Alkali mai shari’a Oludotun Adefope-Okojie ta tabbatar da matakin da jami’ar jihar Abia ta dauka tun 2013.

Shekaru takwas da suka wuce wannan jami’a ta jiha ta karbe digirin da ta ba Uzor Kalu saboda zargin sata da sabawa ka’idojin jami’ar da yake makarantar.

Tsohon Gwamnan Abia
Sanata Orji Uzor Kalu Hoto: @orji.kalu.79
Asali: Facebook

Uzor Kalu ya dace a kotun tarayya

‘Dan siyasar ya kai maganar gaban babban kotun tarayya, inda ya dace a ka ba shi gaskiya. A jiya ne kotun daukaka kara ta soke nasarar da Sanatan ya samu.

A sabon hukuncin da aka yi, an rusa shari’ar kotun Isikwuato da ta dawowa tsohon gwamnan da digirinsa. Kalu ya yi mulki a Abia ne tsakanin 1999 da 2007.

Alkalin kotun daukaka kara da ke jihar Imo, Oludotun Adefope-Okojie ta ce wanda ya saurari karar a baya, bai da hurumin tsoma baki a wannan magana.

Kara karanta wannan

Yan bindiga da Sojojin sun yi musayar wuta a Imo kan umarnin zama a gida na IPOB

Jami'ar ABSU ta yabawa alkalanci

Lauyan da ya tsayawa jami’ar ABSU a kotu, Jesse Nwaenyo yace sun ji dadin wannan hukunci da ya tabbatar da cewa Kalu bai cancanta da digirin makarantar ba.

The Whistler tace daga cikin dalilan karbe takardar karatun ‘dan siyasar shi ne zango biyu kawai ya halarta a lokacin da yake dalibi, a maimakon zango shida.

Sata ta saci sata?

An ji Abubakar Malami ya bukaci a binciki zargin yin gwanjon gidaje, motoci da filayen sata da gwamnatin Muhammadu Buhari ta karbo a hannun barayin kasa.

Kwamitin da Mai girma Ministan ya kafa zai gano ko da gaske ne an sa wadannan kaya a kasuwa ta karkashin kasa kamar yadda ake ji rade-radi su na yawo.

Asali: Legit.ng

Online view pixel