Sata ta saci sata: Minista ya kafa kwamitin binciken zargin satar dukiyar barayin Gwamnati

Sata ta saci sata: Minista ya kafa kwamitin binciken zargin satar dukiyar barayin Gwamnati

  • Ana rade-radin cewa wani jami’in gwamnati yana yin gwanjon kadarorin da aka karbo daga barayi
  • Ministan shari’a, Abubakar Malami SAN ya kafa kwamiti na musamman domin binciken wannan zargi
  • AGF yace gwamnatin tarayya ba ta fara saida kayan da aka karbe a hannun marasa gaskiya ba tukuna

Abuja - Ministan shari’an Najeriya, kuma babban lauyan gwamnatin tarayya, Abubakar Malami, ya kafa kwamiti da zai binciki zargin saida kadarorin sata.

Jaridar Premium Times ta fitar da rahoto a ranar Talata, 30 ga watan Nuwamba, 2021, cewa Ministan shari’a ya kafa kwamiti da zai binciki wannan zargi.

Abubakar Malami SAN ya bayyana cewa gwamnatin Muhammadu Buhari ba ta fara saida kadarorin da ta karbo a hannun barayin gwamnati ba tukuna.

A wani jawabi da Ministan ya fitar ta bakin mai magana da yawunsa, Dr. Umar Gwandu, ya ce ya ji rade-radin wani jami’in gwamnati yana gwanjon kayan satan.

Kara karanta wannan

Yawan 'yan Najeriya na bamu tsoro, dole mu yi wani abu, inji gwamnatin Buhari

Umar Gwandu ya bayyana gwamnatin tarayya ta kafa kwamiti da zai yi bincike na musamman.

Ministoci
AGF Abubakar Malami da Babatunde Raji Fashola Hoto: @umar.j.gwandu
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Ya kamata a bayyana gaskiyar magana, ofishin Ministan shari’an Najeriya, kuma babban lauyan gwamnatin tarayya, bai fara saida kadarorin gwamnati ba.”
“Mai girma AGF, Abubakar Malami SAN, ya kafa kwamitin mutum biyar da zai binciki gaskiyar wannan rade-radi da yake yawo cewa wani jami’in ma’aikatar shari’a ya saida kadarorin da aka karbo ba tare da sanin Ministan shari’a ba.” – Umar Gwandu.

Yadda kwamitin zai yi aiki

Rahoton yace mai magana a madadin Ministan yace an aika takarda a game da batun zuwa ga lauyan gwamnatin tarayya, Umar Mohammed tun a ranar Litinin.

Wasikar ta bukaci Umar Mohammed ya binciki sahihanci ko rashin ingancin wannan labari.

Gwandu yace Darektan tuhuma na tarayya ne zai jagoranci aikin wannan kwamiti da aka kaddamar a ranar Talata, inda aka bukace shi ya yi aiki da doka.

Kara karanta wannan

Atiku ya ba APC shawara ta dauki kwas a wajen Gwamonin PDP, ya caccaki duka Jihohin APC

Ana sa ran kwamitin zai kammala aiki nan da mako guda, daga nan sai a tura rahoto zuwa ga lauyan gwamnati da sakataren din-din-din na ma’aikatar shari’a.

A makon nan ne aka ji daya daga cikin jiga-jigan PDP a Kudancin Najeriya, Raymond Dokpesi ya ce a halin da ake ciki, al’umma sun kagara PDP ta koma kan mulki.

Raymond Dokpesi ya zargi gwamnatin Muhammadu Buhari da rusa tattalin arziki, yace dama sun san APC karya take yi wa mutane, ba za ta iya rike Najeriya ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel