Yanzu-Yanzu: Buhari ya bada umurnin a buɗe wa 'yan Nigeria Twitter, amma da sharaɗi

Yanzu-Yanzu: Buhari ya bada umurnin a buɗe wa 'yan Nigeria Twitter, amma da sharaɗi

  • Daga karshe, Shugaba Muhammadu Buhari ya bada umurnin a dage daktarwar da aka yi wa Twitter a Nigeria
  • Buhari ya bada sanarwar hakan ne yayin jawabinsa na ranar 'yancin kasa ta 1st Otober ta shekarar 2021 yayin da kasar ke cika shekaru 61 da samun yanci
  • Shugaban kasar ya ce kwamitin da ya kafa ta tattauna da Twitter sun kuma cimma matsaya don haka ya ce a dage dakatarwar yayin da kamfanin zata cika sharrudan

FCT, Abuja - Shugaba Muhammadu Buhari, a ranar Juma'a, ya ce ya bada umurnin a dage dakatarwar da aka yi wa shafin Twitter a Nigeria tun watan Yunin 2021.

The Punch ta ruwaito cewa Buhari ya bayyana hakan ne yayin jawabin da ya yi wa 'yan Nigeria na ranar bikin samun 'yancin kasa karo na 61.

Kara karanta wannan

Telegram ta yi fintinkau yayin da Facebook, WhatsApp da Instagram suka daina aiki

Yanzu-Yanzu: Buhari ya bada umurnin a buɗe wa 'yan Nigeria Twitter, amma da sharaɗi
Yanzu-Yanzu: Buhari ya bada umurnin a buɗe wa 'yan Nigeria Twitter, amma da sharaɗi
Asali: Original

Ya bayyana cewa kafafen sada zumunta na da amfani amma ya yi koka kan yadda wasu ke amfani da kafar don shirya muggan ayyuka da watsa labaran karya da kabilanci da tada rikicin addini.

Shugaban kasar ya ce:

"Kafar sada zumunta na da amfani sosai kuma ya bawa miliyoyin yan Nigeria daman yin zumunci da kasuwanci da samun labarai da wasu bayanai.
"Amma, abubuwan da suka faru a baya-bayan nan sun nuna ba wai kafa bane kawai na watsa bayanai.
"Wasu na amfani da shi ta hanyar da bai dace ba don shiryawa da aikata miyagun ayyuka, watsa labaran karya da kyamatan juna saboda banbancin kabila da addini.
"Don magance wannan matsalolin, gwamnatin tarayya ta dakatar da Twitter a Nigeria a ranar 5 ga watan Yunin 2021 don bawa gwamnati damar daukan matakan magance wadannan kallubalen.

Kara karanta wannan

Labarin gimbiyar da ta bar masarautarsu ta auri talaka ya dauki hankalin jama'a

"Bayan dakatar da shafin Twitter, kamfanin Twitter ya tuntubi gwamnatin Nigeria don warware matsalar. Daga bisani, na kafa kwamitin shugaban kasa don tattaunawa da Twitter don warware matsalar.
"Kwamitin ya gana da Twitter don duba wasu abubuwa masu muhimmanci. Abubuwan sune tsaron kasa da hadin kan kasa; Rajitsa, Bude Ofishi a Nigeria da wakilci; Haraji; Warware matsaloli; Tallata abubuwan gida Nigeria.
"Bayan tattaunawa mai tsawo, an warware lamuran kuma na bada umurnin a dage dakatarwar da aka yi wa Twitter amma idan an cike sharrudan domin bawa yan kasarmu damar cigaba da yin amfani da shafin don kasuwanci da abubuwa nagari.
"A matsayin mu na kasa, za mu tabbatar cewa kamfanonin sadarwar zamani na amfani da kafarsu don inganta rayuwarmu, girmama 'yancin Nigeria, al'adunta da tsaro a yanar gizo."

Pantami na neman ganin a sauƙaƙa wa 'yan Nigeria kuɗin data

A wani labarin daban, Ministan Sadarwa da tattalin arzikin zamani, Isa Ali Pantami, a ranar Alhamis, ya bayyana shirin gwamnatin tarayya na ganin ta saukaka farashin kudin data don shiga intanet, The Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Hoton tsohon rasit da ke nuna an siya buhu 40 na siminti kan N1520 ya janyo cece-kuce

Pantami, wanda ya bayyana hakan a ranar Alhamis yayin wani taro da aka yi na Intanet a Abuja ya kara da cewa gwamnatin tana aiki don ganin farashin data/intanet ya yi sauki ta yadda talaka sai iya siya.

Ministan ya ce ana aiki don magance abubuwan da ke saka kudin data tsada da suka hada da tsaro da fasahar sadarwar da sauransu

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164