Bankin Afrika zai ba Gwamna Ganduje Dala miliyan 110 domin ayi ayyuka a kauyukan Kano

Bankin Afrika zai ba Gwamna Ganduje Dala miliyan 110 domin ayi ayyuka a kauyukan Kano

  • Babban bankin cigaban Afrika zai ba Najeriya tallafin Dala miliyan 563 domin bunkasa kauyuka
  • Shugaban AfDB, Dr. Akinwumi Adesina ne ya bayyana wannan a lokacin da ya ziyarci jihar Kano
  • Dr. Akinwumi Adesina yace jihar Kano za ta samu $110m daga wannan tallafi, kimanin N45bn kenan

Kano - A yunkurinsa na samar da abubuwan more rayuwa a Najeriya, babban bankin cigaban Afrika na AfDB, zai ba gwamnatin tarayya Dala miliyan 563.

Jaridar The Cable ta fitar da rahoto a ranar Talata, 23 ga watan Nuwamba, 2021, inda ta ce shugaban bankin AfDB, Dr. Akinwumi Adesina ne ya fadi haka.

Akinwumi Adesina ya kai wa gwamnan jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ziyara ta musamman, inda ya shaida masa jiharsa za ta samu wannan kudi.

Adesina yace za a ba gwamnatin Kano fam miliyan 110 daga cikin kudin da aka warewa kasar.

Kara karanta wannan

Abin da ya sa Gwamnati ba ta isa ta rabawa Talakawa kudi idan an cire tallafi ba - ‘Yan Majalisa

Ina za a kai kudin?

Za a kashe wannan kudi fam Dala miliyan 563 ne wajen samar da hanyoyi a kauyuka, da inganta sha’anin sufuri da kuma samar da ruwan sha mai tsabta a Najeriya.

Bankin Afrika zai ba Gwamna Ganduje Dala miliyan 110 domin ayi ayyuka a kauyukan Kano
Dr. Akinwumi Adesina Hoto: @Akin_Adesina
Asali: Twitter

Punch tace uwa-uba, za ayi amfani da kudin wajen bunkasa harkar noma a jihohin kasar nan.

Kano ta tashi da kusan 20%

“Za mu kashe Dala miliyan 110 a Kano a shirinmu na aikin gona na musamman. Gaba daya mu na da Dala miliyan 563 da aka warewa jihohin kasar nan.” – Adesina.
“A cikin wannan, za a ba jihar Kano har Dala miliyan 110. Ka yi tunanin irin amfanin da wannan kudi zai yi wajen gina tituna a kauyuka, samar da hanyoyi, ruwa da kuma tsabta. Sannan za mu sa kudin a harkar gona domin bunkasa abincin da ake nomawa.”

Kara karanta wannan

Gaba da gaban ta: Bidiyo da hotunan Tinubu ya na jinjina, gurfane gaban Aminu Dantata

A cewar Dr. Akinwumi Adesina tallafin kudin zai taimakawa mutanen jihar Kano wajen samar da ayyukan yi a dalilin bunkasa tattalin arzikin kauyuka da harkar noma.

Da wannan tsari, Adesina yace daloli za su tafi wajen gina abubuwan more rayuwa a karkara. Ta haka za a rage asarar abinci, a kara yawan arzikin da jihar ta ke da shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel